BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Quoll: Dabbar da ke haƙura da bacci saboda jima'i

Namijin dabbar quoll

Wed, 1 Feb 2023 Source: BBC

Namijin dabbar quoll na haƙura da bacci domin samun ƙarin jima'i - kuma hakan zai iya kashe shi, kamar yadda wani bincike da aka gudanar a Australia ya bayyana.

Binciken ya gano cewa mazan quoll ɗin na tafiya mai tsawo domin neman macen dabba domin jima'i, wanda hakan ya sa suke haƙura da bacci.

Ƙarancin baccin da suke yi ya ƙara fito da bayanai da ke nuna irin waɗannan dabbobin na Australia masu cin nama kan cewa suna jima'i har su kashe kansu, kamar yadda wani masani ya bayyana.

"Suna tafiya mai tsawo domin su je su yi jima'i kuma da alamu suna haƙura da baccin da ya kamata su yi inda suke neman mace," in ji Christofer Clemente, wani babban malami a Jam'iar Sunshine Coast.

Jami'ar ce ta jagoranci wannan bincike da haɗin gwiwar Jami'ar Queensland. An wallafa binciken ne a ranar Laraba.

Masu bincike sun tattara bayanai na tsawon kwanaki 42 ta hanyar saka na'ura a bayan maza da matan dabbobin na quoll a Groote Eylandt, wanda wani tsibiri ne da ke gaɓar tekun Australia ta arewa.

Wasu daga cikin dabbobin na quoll da aka yi bincike a kansu sun yi tafiyar sama da kilomita goma a cikin dare guda, wanda hakan ke nufin sun yi tafiyar sama da kilomita 40 a irin tafiyar bil adama.

Haka kuma binciken ya nuna maza daga cikinsu sun fi jawo hankalin ƙwari.

Dalilin hakan da ake ganin ya fi zama sahihi shi ne ba su mayar da hankali sosai wurin raino. Masu bincike sun ce mazan ba su cika lura da mayar da hankali wurin neman abinci kamar matan bako kauce wa dabbobi masu cutar da su.

"Ƙarancin bacci da kuma alamomi da ke da alaƙa da hakan na sakawa warkewa daga ciwo ke da wahala, hakan kuma kan yi bayani kan dalilan mace-macen da ake samu a mazan bayan an yi jima'i," in ji Joshua Gaschk, wanda ya jagoranci binciken.

"Ba wahala sun zama abin da za a kama, ba za su iya guje wa mota ta buge su ba, ko su mutu sakamakon gajiya." in ji shi.

Hukumar da ke kula da dabbobin daji ta Australiya ta bayyana cewa akwai dabbobin quoll 100,000 da suka rage kuma suke raguwa.

Haka kuma rasa mazauni da hari da magunan kan titi ke kai musu duk na ja suna mutuwa, haka kuma suna fuskantar barazana daga gubar da ƙwado ke fitarwa.

Source: BBC