Rasha ta fara kwashed ubun-dubatar fararen hula da kuma shugabannin yankin Kherson da ta naɗa a garin da ke kudancin Ukraine, wanda ta mamaye. Shugaban yankin mai suna Vladimir Saldo ya ce dukkan ma'aikatun da Rashar da sahe-sashe za su tsallaka zuwa gaɓar Kogin Dnieper. Mutum kimanin 50,000 zuwa 60,000 ne ake sa ran za su fice daga yankin "cikin rukuni-rukuni kuma sannu a hankali," a cewarsa. Ukraine na kira ga mazauna yankin da su bijire wa yunƙurin na Rasha. Shugaban gwamnatin na Kherson ya ce Rasha na son kwace fararen hular ne saboda ta yi amfani da su a matsayin garkuwa. Ana kallon kwashe fararen hula da wata ƙasa da ke kai hari za ta yi a daga wani yanki da ta mamaye a matsayin laifin yaƙi. Cikin wani mataki na gaggawa, Shugaban Rasha Vladmir Putin ya ce ya saka hannu wata doka da soja kan yankuna huɗu na Ukraine ɗin da suka haɗa da Kherson, wanda Rashar ta ƙwace a watan da ya gabata. An ga mutane sun taru kusa da Dnieper cikin wani bidiyo da gidan talabijin na Rasha ya nuna ranar Laraba, yayin da suke bin layin hawa jiragen ruwa. Sai dai ba a san ko su nawa ba ne da ke son barin yankin. Wata mazauniyar Kherson ta faɗa wa BBC cewa ba za ta je ko'ina ba har sai sojojin Ukraine sun ƙace shi daga hannun na Rasha: "Mutane ba a firgice suke ba, ba wanda ke son a ɗauke shi." Ta ƙara da cewa yanzu sojojin Rasha neman gidan ɓuya suke a garin. "Akwai su da yawa a nan, shigar fararen hula suke yi. Muna iya ganin su - sun fita daban da mutanen Kherson. Suna tafiya cikin rukuni, sun rage tsayin gashin su kuma sun fi saka baƙaƙen kaya."