Menu

Rabon tallafin rage raɗaɗin ƙara kuɗin mai ya janyo taƙaddama a Najeriya

Majalisar dokokin Najeriya a Abuja

Fri, 14 Jul 2023 Source: BBC

Bayan da Majalisar Dokokin Najeriya ta amince da bukatar shugaban kasar Bola Ahmad Tinubu, ta neman Naira biliyan 500 don rage radadin cire tallafin man fetur da gwamnatinsa ta yi, yanzu haka ana ci gaba da bayyana ra'ayoyi masu cin karo da juna kan yadda tallafin zai shafi jama'a.

Ita dai gwamnatin shugaban kasar ta tsara cewa za ta rika biyan kimanin mutum miliyan 12 tallafin Naira dubu takwas a duk wata har tsawon watanni shida, domin ganin kudin ya zagaya, arziki ya karu a tsakanin jama'a.

Sai dai wasu daga cikin 'yan jam'iyyarsa ta APC na ganin ko a gwamnatin baya ta tsohon shugaban kasar Muhammadu Buhari an gwada irin wannan, amma bai yi wani tasiri ba.

Injiniya Sani Bala Tsanyawa, wani dan majalisar wakilai daga jihar Kano, ya shaida wa BBC cewa sun amince da bukatar ne saboda wannan na daya daga cikin bukatun shugaban na farko, amma ba ya ji hakan zai yi wani tasiri.

A cewarsa: ''Abun a yaba ne farawar da aka yi, amma ko cewa aka yi mutum na daukar albashi ka kara masa Naira dubu takwas, babu wani abu da za ta masa, ballantana kuma mutumin da ko yaushe yana gida babu abun da yake yi.

''Wannan adadi ko kashi goma na 'yan Najeriya bai kai ba, mutum miliyan goma sha biyu cikin sama da talakawa miliyan dari da hamsin ai ka ga babu abin da aka yi'' in ji shi.

Ya nanata cewa akwai bukatar a ce wannan adadi ya fi haka, duba da cewa lamarin ya shafi kowa da kowa ne.

Me jama'a ke cewa?

BBC ta tattauna da wasu mutane da dama a Najeriya don jin ra'ayoyinsu kan wannan al'amari, sai dai yawancinsu na nuna goyon bayansu ne ga duk wani abu da zai zamanto maslaha ga jama'a.

Wani mutum da muka zanta da shi a Abuja, ya ce ''Ba mu da mota ba mu da kudin mai, inda muke biyan Naira dari yanzu Naira dari uku, abun ya shafe mu kwarai da gaske''

''Kare ana biki a gidansu ya ce mu gani a kasa'', in ji ra'ayin wani mutum na daban da shi ma muka zanta da shi

Hatta masu sayar da abinci wadanda harkarsu ta samu nakasu sakamakon yadda farashin komai ya daga na sa ran wannan tallafi zai kai gare ku.

Ita dai gwamnatin Shugaba Tinubu ba ta fito karara ta yi maganar ga lokacin da za a fara rabon ba, sai dai tuni matasa suka yi kwanto suna jira don cin gajiyar shirin da zarar an fara.

Gwamnatocin da suka gabata na baya ma a Najeriya sun yi wani abu makamancin iran haka, sai dai daga bisani ya kai ga lalacewa ba tare da an ga tasirin hakan ba.

Source: BBC