Hukumar Hisbah a jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta ce ta kama wasu matasa da tsakar rana suna cin abinci, abin da ke nuna ba sa yin azumi.
Shugaban hukumar, Dr. Aliyu Musa Kibiya, ya shaida wa BBC cewa wadanda aka kama sun hada da maza uku da mata takwas.
A cewarsa, sun kama mutane ne a wurare daban-daban a jihar, yana mai cewa rashin yin azumin abin takaici ne.
"Mun kamo mutum 11 - mata takwas, maza hudu wadanda aka same su a cikin wannan yanayi. Za mu tantance wala'alla wani yana da wani uzurin da idan mun kalla mun ga karbabben uzuri ne shikenan; wanda kuma aka ga haka nan ya yi irin wannan dabi'ar sai a bi matakai wajne yi masa nasihohi da kuma duk abin da ya kamata na bin doka da hukunta shi," in ji Dr. Kibiya.
Shugaban na Hisba ya ce bai kamata a ga "mace a bainar jama'a kin zo kina cin abinci ba, komai uzurinki."
Ya kara da cewa hukumarsa za ta ci gaba da kama duk wanda ta gani yana ci abinci a lokacin azumi.
Duk masu irin wannan halayyar a cikin mutane, ba sa kunyar Allah ba sa kunyar mutane, lallai za mu ci gaba da bibiyarsu ana daukar matakin da ya dace," a cewar Dr. Kibiya.
Wasu mazauna jihar ta Kano suna goyon bayan irin wannan mataki yayin da wasu ke ganin hakan bai kamata ba kasancewa Musulunci ya bai wa wasu rukunai na mutane damar sauke azumi, kana bai tilasta musu cin abinci a boye ba.
A kowacce shekarar hukumar ta Hizbah na gudanar da irin wannan kame a cikin birni da kanana hukumomin Kano.
Azumi dai wajibi ne kan duk wani musulmi baligi mai cikakken lafiya a watan Ramadan, sai dai idan akwai dalili mai ƙarfi ko uzuri ga mata masu haila ko tsoffi da ba sa jure yunwa.