Menu

Rasha ta kai hari wuri mai tarin jama'a a Ukraine

Sojojin Rasha

Sun, 2 Jul 2023 Source: BBC

Rasha ta kai hari da wasu makamai masu linzami biyu tsakiyar birnin Kramatorsk da ke gabashin yankin Donetsk a Ukraine.

Jami’ai sun ce harin ya hallaka akalla mutum hudu da suka hada da wata yarinya mai shekara 17.

Harin ya kuma raunata mutum 40 ciki har da wani jariri dan wata 8, da kuma wasu ‘yan kasashen waje uku.

Harin na makami mai linzami ya fada kan wani yanki ne na wani kanti da ake siyayya da kuma wani gidan cin abinci a daren Talata.

Ofishin babban mai gabatar da kara ya ce akwai gidajen da jama’a ke zaune a tsakiyar inda makaman suka fada wa.

Rahotanni sun ce hukumomin tsaro sun kai dauki wajen a lokacin , inda aka rika kwashe jama’ar da harin ya rutsa da su.

Ana ganin akwai wasu mutanen da ke karkashin buraguzai.

Hukumomin yankin sun ce waje ne da yake da yawan jama’a farar hula.

Wani da ya ga harin ya gaya wa BBC cewa yana iya jin mutane na kara, yayin da masu ceto ke kokarin kaiwa garesu.

Mutumin ya yi kiyasin cewa akwai ma’aikata kusan 80 da masu sayayya a gidan cin abincin a lokacin harin.

Saboda haka yake ganin yawan wadanda harin ya rutsa da su kai iya zarta yadda aka fada sosai.

Wata matashiya da ke wajen aikin ceton ta bayyana abin da ta gani, inda wata mata da ba a kai ga gane ta ba take bayani kan yadda harin ya rutsa da ita.

Inda take cewa, ‘’ba zan iya tuna komai ba. Haske kawai na gani.’’

Hotunan da jama’a ke yadawa da kuma wadanda aka dauka da ‘yan kananan jiragen sama da ake sarrafawa daga kasa na nuna yadda gine-ginen wajen suka lalace sosai wasu ma sun ruguje gaba daya.

Masu agaji sun kewaye wajen inda suke kwashe buraguzai suna mika wa juna yayin da suke kokarin gano mutane.

Suna yi wa mutane tsawa kan su yi shiru ko za a ji wadanda buraguzai suka danne.

Daman Rasha ta saba harar birnin na Kramatorsk da makamai masu linzami . Domin ko a watan Afirilu da bara wai hari da Rsaha ta kai ta sama a kan tashar jirgin kasa ta birnin ya hallaka sama da farar hula 60 da raunata wasu sama da 120.

Birnin mai jama’a wajen 150,000 na daya daga cikin manya da har yanzu ke hannun Ukraine, a wadanda suke gabashin kasar da Rasha ta mamaye, kuma yana da tazarar kilomita 30 ne kawai daga fagen daga.

Source: BBC