An bai wa dan kwallon Manchester United, Marcus Rashford kyautar gwarzon dan kwallon gasar Firemiya na watan Fabarairu, kyauta a karo na uku a kakar wasa ta bana.
Hakan ya sa Rashford ya kamo bajintar Mohamed Salah na Liverpool.
A kakar wasa ta 2017 zuwa 2018 ne Salah ya kafa tarihi a gasar.
Rashford ya lashe kyautar a watan Satumba da Junairu da kuma Fabarairu.
Shi ma Erik ten Hag ya samu kyautar manaja mafi bajinta a karo na biyu.
Rashford ya zura kwallo 26 a kakar wasa ta bana kuma shi ne dan kwallo na farko da ya ci kyautar sau biyu a jere tun bayan Ilkay Gundogan na Manchester City a watan Janairu da Fabarairun 2021.
Ten Hag, wanda ya lashe kyautar a watan Satumba da Fabarairu ya jagoranci United ta lashe gasar EFL a bana. Kofi na farko a cikin shekaru shida.