Menu

Rashford zai ci gaba da taka leda a United zuwa 2028

Marcus Rashford

Wed, 19 Jul 2023 Source: BBC

Marcus Rashford ya saka hannu kan yarjejeniyar da zai ci gaba da taka leda a Manchester United zuwa karshen 2028.

Mai shekara 25 ya dade yana tattaunawa da mahukuntan kungiyar kan batun tsawaita zamansa a Old Trafford, bayan da yarjejeniyarsa za ta kare a karshen kakar 2024.

Dan wasan tawagar Ingila ya taka rawar gani a karkashin Erik ten Hag a kakar da ta wuce, inda ya ci kwallo 30 a karawa 56 da ya yi mata.

Tun bayan da ya fara yi wa United wasa a 2016 a karawa da Midtjylland, kawo yanzu ya ci kwallo 123 a fafatawa 359.

Rashford ya ji rauni a allon kafada a Agustan 2021, inda ya ci kwallo biyar a kakar karshe da Ole Gunnar Solskjaer ya ja ragamarr United.

Daga baya Ingila ba ta gayyace shi wasa hudu da ta kara a Nations League a Yunin 2022 ba.

Rashford ya koma kan ganiya a kakar da ta wuce tun bayan rawar da ya taka a gasar kofin duniya da aka buga a Qatar a 2022.

Ya bayar da gudunmuwar da United ta samu gurbin buga Champions League a kaka mai zuwa, bayan da ya ci kwallo da kungiyar ta dauki Carabao Cup, bayan ta doke Newcastle United.

Source: BBC