Menu

Ratcliff ya sake komawa batun sayen Manchester United

42634900 Filin wasan Manchester United

Wed, 18 Jan 2023 Source: BBC

Kamfanin Ineos na attajiri dan Birtaniya, Sir Jim Ratcliff ya sanar cewar ya nuna sha'awar sayen Manchester United.

Cikin watan Nuwamba iyalan Glazer suka sanar cewar suna duba hanyar da za su sayar da kungiyar ta Old Trafford.

A bara ne Ratcliff ya taya Chelsea fam biliyan 4.5, bayan da Roman Abromovich ya saka kungiyar a kasuwar, amma ba a sayar masa ba.

Kamfaninsa na Ineos mai hada-hadar man fetur kan yi cinikin fam biliyan 50 a duk shekara, mai ma'aikata 26,000 a kasashe 29 a fadin duniya.

Bayan da ba a sayar masa da Chelsea ba, Ratcliff ya tattauna da Joel da kuma Avram Glazer kan cinikin United, wadanda suka ce ba za su sayar masa ba.

Daga baya iyalan Glazer suka sauya shawara, dalilin da Ratcliff ya sake komawa zawaracin United.

Rukunin Ineos shi ne ya mallaki Nice mai buga Ligue 1 a Faransa da Lausanne ta Switzerland.

Haka kuma Ineos yana da hadin gwiwar kasuwanci da Marsandi a gasar tseren motocin Formula 1 da tawagar tseren kekuna ta Team Sky ta Birtaniya tun daga 2019.

Iyalan Glazer sun mallaki Manchester United tun daga 2005.

United tana ta hudu a teburin Premier League, bayan da kungiyar ke kokari karkashin Erik ten Hag, wanda ya karbi aikin a farkon kakar nan.

Source: BBC