BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Real Madrid ta yi rashin nasara a gidan Valencia a La Liga

Yan wasan Real Madrid

Sun, 21 May 2023 Source: BBC

Valencia ta ci Real Madrid 1-0 a wasan mako na 35 a gasar La Liga da suka kara ranar Lahadi.

Mai masaukin baki ta zura kwallo a raga a minti na 33 ta hannun Diego Lopez Noguerol, wanda ya samar mata maki ukun da take bukata.

An bai wa Vinicius Junior jan kati a wasan, wanda magoya bayan Valencia suka yi ta masa kalaman wariya.

Da wannan sakamakon Valencia ta bar kasa-kasan teburin La Liga ta yi sama zuwa ta 13 da makinta 40.

Ita kuwa Real Madrid wadda ta yi rashin nasara karo na takwas a bana a La Liga ta koma ta ukun teburi da maki 7i, Atletico ce ta biyu mai 72.

Tuni dai Barcelona ta lashe kofin kakar bana.

Real Madrid, wadda ta dauki Uefa Super Cup da Fifa World Club Cup da Copa del Rey a bana ta rasa Champions League, bayan da Manchester City ta fitar da ita.

Real ce mai rike da Champions League na bara na 14 jimilla, kuma ita ke rike da La Liga, wanda Barcelona ta karbe daga wajenta.

Karo na uku da suka fuskanci juna a bana kenan:

Sifanish La Liga Lahadi 21 ga watan Mayun 2023

  • Valencia 1 - 0 Real Madrid
  • Sifanish La Liga Alhamis 2 ga watan Fabrairun 2023

  • Real Madrid 2 - 0 Valencia


  • Sifanish Super Cup Laraba 11 ga watan Janairun 2023

  • Real Madrid 1 - 1 Valencia


  • Sauran wasannin da suka rage wa Real a La Liga:

    Sifanish La Liga Laraba 24 ga watan Mayu

  • Real Madrid da R. Vallecano


  • Sifanish La Liga Asabar 27 ga watan Mayu

  • Sevilla da Real Madrid


  • Sifanish La Liga Lahadi 4 ga watan Yuni

  • Real Madrid da Ath Bilbao


  • Source: BBC