Menu

Real Madrid za ta ɗauki Kane madadin Benzema

Harry Kane

Mon, 5 Jun 2023 Source: BBC

Harry Kane yana cikin jerin 'yan wasan da Real Madrid ke son zaɓar wanda zai maye gurbin Karim Benzema.

Kane, mai shekara 29, yana da sauran ƙunshin kwantiragin kaka ɗaya da ta rage masa a Tottenham, wanda bai fayyace makomarsa ba kawo yanzu.

Benzema wanda ya bar Real Madrid, bayan shekara 14 a Santiago Bermabeu, ya bar gurbin da ƙungiyar ya kamata ta cike kafin fara kakar baɗi.

Sauran 'yan wasan da Real ke son tuntuɓa sun haɗa da ɗan wasan Napoli, Victor Osimhen da na Inter Milan, Lautaro Martinez da na Chelsea, Kai Havertz da kuma na Juventus, Dusan Vlahovic.

Real mai kofin zakarun Turai 14 ta daɗe tana son ɗaukar Kane, bayan da fitattun 'yan kwallonta da yawa ke shirin barin Bernabeu a ƙarshen kakar nan.

Bayan Benzema da zai bar Real Madrid a kakar nan, sauran sun hada da Eden Hazard da Marco Asensio da kuma Mariano Diaz.

Idan waɗannan 'yan wasan suka bar Real, ƙungiyar za ta samu rarar fam miliyan 77 da take biyansu ladan wasa da albashi da sauran tsarabe-tsarabe.

Har yanzu Real Madrid na ci gaba da tattaunawa da Borussia Dortmund kan ɗaukar Jude Bellingham.

Shugaban Tottenham, Daniel Levy na fatan Kane zai ci gaba da taka leda a ƙungiyar, amma sai Real ta biya fam miliyan 100 kafin ta bari ɗan kwallon ya bar Tottenham.

Kane ya ci kwallo 280 a wasa 435, kuma saura kwallo 47 tsakaninsa da yawan ta Alan Shearer a Premier League na farko a cin kwallaye a gasar mai 260.

Benzema, wanda ke riƙe da Ballon d'Or, mai shekara 35, ya koma Real Madrid daga Lyon a 2009, inda ya lashe Champions Leagues biyar da La Liga huɗu a Madrid.

Source: BBC