BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Real na shirin karawa da Girona a La Liga ranar Talata

23502954 Hoton alama

Tue, 25 Apr 2023 Source: BBC

Real Madrid na shirye-shiryen fafatawa da Girona a wasan mako na 31 a La Liga ranar Talata.

Kungiyar Santiago Bernabeu ta ci Celta Vigo 2-0 a karawar mako na 30, yanzu kuma za ta ziyarci Montilivi domin buga wasan mako na 31 a babbar gasar tamaula ta Sifaniya.

Tun da sanyin safiya 'yan wasan Real Madrid suka fara da motsa jiki da guje-guje, sannan aka raba tamaula, bayan da aka raba filin gida biyu.

An karkare da buga wa gola tamaula, yayin da Mendy da Alaba suka motsa jiki a rufafen daki a shirin da suke na murmurewa daga jinya.

Real Madrid da Girona sun tashi 1-1 a wasan farko a bana a La Liga ranar 30 ga watan Oktoba a Santiago Bernabeu.

Vinicius Junior ya fara cin kwallo a minti na 70, yayin da Girona ta farke saura minti 10 a tashi daga wasan ta hannun Cristhian Stuani a bugun fenariti.

A karawar ce aka bai wa Toni Kroos jan kati daf da za a busa tashi daga wasan.

Real Madrid tana ta biyu a teburin La Liga da maki 65, inda Barcelona ce ta daya mai maki 76.

Ita kuwa Atletico Madrid tana ta uku a teburin La Liga da tazarar maki biyar tsakaninta da Real Madrid ta biyu.

Wasannin da za a buga ranar talata 25 ga watan Afirilu:

  • Cadiz da Osasuna
  • Girona da Real Madrid


  • Real Betis da Real Sociedad


  • Source: BBC