BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Real za ta kara da Atletico a Spanish Super Cup

25826282 Hoton alama

Wed, 25 Oct 2023 Source: BBC

Real Madrid za ta kece raini da Atletico Madrid a Spanish Super Cup a zagayen daf da ƙarshe a Saudi Arabia.

Daya karawar za a yi ne tsakanin Barcelona da Osasuna kamar yadda hukumar kwallon kafar Sifaniya ta sanar ranar Laraba.

Real Madrid mai riƙe da Copa del Rey za ta kara da Atletico a Riyadh ranar 10 ga watan Janairu.

Ita kuwa Barcelona, wadda ta lashe La Liga a bara za ta yi gumurzu da Osauna, ranar 11 ga watan Janairun 2024

Za a buga wasan ƙarshe ranar 14 ga watan Janairu a filin wasa na Al-Nassr Al-Awwal Park Stadium da ke birnin Saudi.

Al-Nassr ita ce ƙungiyar da tsohon ɗan wasan Real Madrid, Cristiano Ronaldo ke taka leda tare da Sadio Mane da kuma Amyeric Laporte.

Hukumar kwallon kafa ta Sifaniya ta mayar da buga Super Cup dinta ga Saudi Arabia a 2019, tun daga lokacin aka ci gaba da gudanar da gasar, illa 2020/21 saboda cutar korona.

Source: BBC