BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Real za ta kara da Chelsea da kwarin gwiwa a Champions

12869172 Yan wasan Real Madrid

Sun, 16 Apr 2023 Source: BBC

Real Madrid ta je ta doke Cadiz 2-0 a wasan mako na 29 a gasar La Liga da suka kara ranar Asabar.

Nacho Fernandez ne ya fara cin kwallo a minti na 72 da take leda, sannan minti hudu tsakani Marco Asensio ya kara na biyu.

Real Madrid mai rike da La Liga na bara tana ta biyu a teburin bana da maki 62, yayin da ranar Lahadi, Barcelona mai maki 72 ta je gidan Getafe buga karawar mako na 29.

Wannan nasarar da Real ta yi ranar Asabar zai kara mata karfin gwiwa a wasa na biyu a Champions League da za ta ziyarci Chelsea ranar Talata 18 ga watan Afirilu.

Kungiyar Sifaniya ta doke ta Ingila 2-0 a wasan farko zagayen quarter finals da suka kece raini a Santiago Bernabeu ranar 12 ga watan Afirilu.

Real mai Champions League na bara mai 14 jimilla ta ci kwallayen ta hannun Karim Benzema da kuma Marco Asensio.

Chelsea mai kofin zakarun Turai biyu ta karasa wasan da 'yan kwallo 10 a fili, bayan da aka bai wa Ben Chilwell jan kati a Sifaniya.

Ranar Asabar Chelsea ta yi rashin nasara 2-1 a Stamford Bridge a hannun Brighton a wasan mako na 31 a Premier League.

Karo na uku da aka ci Chelsea a jere, bayan da Frank Lampard ya sake karbar aikin kociyan kungiyar na rikon kwarya zuwa karshen kakar nan.

Tun bayan da Lampard ya karbi aiki ya sha kashi a hannun Wolverhampton a gasar Premier League karawar mako na 30.

Sai kuma Real Madrid da ta doke Chelsea 2-0 da kuma wanda Brighton ta yi nasara a Premier League ranar Asabar.

Ranar Talata Chelsea za ta san makomarta kan kofin da ya rage mata a gabanta, wato Champions League.

Chelsea tana da maki 39 a mataki na 11 a teburin babbar gasar tamaula ta Ingila, wannan matsayin ba zai kai kungiyar gasar zakarun Turai a badi ba.

Saboda haka cin Champions League ne kadai a bana zai sa kungiyar Stamford Bridge ta samu buga wasannin kakar badi.

Chelsea ba ta samu daukar FA Cup ba, Manchester United ce ta ci Carabao Cup na bana, kenan kungiyar Stamford Bridge ka iya kare kakar nan ba kofi kenan.

Source: BBC