Gwagwarmayar iko tsakanin sojojin Sudan da mayaan rundunar kai ɗaukin gaggawa don tallafawa ayyukan tsaro ta RSF, na ci gaba da gigita Sudan, yayin da fararen hula sama da 50 suka mutu.
Mazauna Khartoum babban birnin ƙasar, sun guje wa harbe-harben makamai, yayin da dakarun RSF ke fafutukar ƙwace fadar shugaban ƙasa da gidan talbijin na ƙasar da kuma shalkwatar sojojin Sudan.
Ƙungiyar likitocin ƙasar ta ce mutum 25 ciki har da fararen hula 17 ne suka mutu a Khartoum.
Rikicin ya ɓarke ne bayan tashin hankali kan shirin miƙa mulki hannun farar hula.
Duk ɓangarorin da ke rikici da juna, sun yi iƙirarin karɓe iko da filin jirgin sama da sauran muhimman wurare a birnin Khartoum, inda aka kwashe tsawon dare ana fafatawa.
Da safiyar Lahadi, an yi ta jin ƙarar harbin makaman atilare a Omdurman da ke maƙwabtaka da Khartoum, da kuma kusa da Bahri.
Aƙalla fararen hula 56 ne aka kashe a birane da jihohin ƙasar, kamar yadda ƙungiyar likitocin Sudan ta bayyana.
Ta ce gomman sojoji sun mutu, wasu kuma ana yi musu magani a asibitoci.
Kungiyar likitocin ta ce aƙalla mutum 595 ne suka jikkata.
Ana dai gwabza faɗan ne tsakanin sojojin da ke biyayya ga shugaban mulkin sojin ƙasar Janar Abdel Fattah al-Burhan, da kuma dakarun RSF masu sanye da kayan sarki ƙarƙashin jagorancin mataimakin shugaban ƙasar Mohamed Hamdan Dagalo, wanda aka fi sani da suna Hemedti.
Hemedti ya ce dakarunsa za su ci gaba da yaƙi, har sai sun ƙwace iko da sansanonin sojin ƙasar.
A nata ɓangare, rundunar sojin Sudan ta ce ta jingine duk wata tattaunawar tsagaita wuta, har sai an rushe rundunar jami'an kayan sarki.
Ƙasashen Burtaniya da Amurka da China da Rasha da Tarayyar Turai sun yi kira a gaggauta kawo ƙarshe faɗan.
Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya yi kira ga Janar Burhan da janar Dagalo su kawo ƙarshen rikicin.