Menu

Rikicin Tigray: Jami'in difilomasiyya na bogi da wasu labaran karya da ke ruruta rikicin Tigray

 117662594 Tigray Banner Gettyimages 1231121976 A watan Nuwambar 2020 ne rikicin ya barke a Habasha sakanin Gwamnati da yan tawayen Tigray

Fri, 26 Mar 2021 Source: BBC

Hankula na ci gaba da tashi a arewacin yankin Tigray na kasar Habasha, inda ake ci gaba da zarge-zargen take hakkin dan adam da hadarin sake shiga wani rikicin.

A watan Nuwambar 2020 ne rikicin ya barke, lokacin da dakarun gwamnatin Habasha suka kaddamar da hare-hare kan 'yan tawayen Tigray da suka karbe iko da sansanin sojin gwamnati da ke yankin.

Yayin da babu wata hanyar shiga yankin sakamakon toshewar da aka yi, sai farfagandar yaki ta barke a shafukan sada zumunta da muhawara daga bangarorin biyu inda suke yada labaran karya kan rikicin.

Jami'an difilomasiyyar Majalisar Dinkin Duniya na bogi

Kamfanin dillancin labarai na Habasha EPA, ya rawaito cewa wani tsohon jami'in Majalisar Dinkin Duniya ya wallafa sakonnin nuna goyon baya ga abin da gwamnatin kasar ke yi.

Shafin Facebook na EPA ya wallafa wani sakon Twitter mai dauke da sunan George Bolton, jami'in Majalisar Dinkin Duniya @GboltonUN.

A sakon Mista Bolton ya bayyana kansa a matsayin mai sharhi kan al'amuran siyasa kuma tsohon jami'in Majalisar Dinkin Duniya, sannan ya bayyana shugabancin yankin Tigray a matsayin na kama-karya, tare da tunawarwa firaiministan kasar ya lashe kyautar Nobel na zaman lafiya, sannan Majalisar Dinkin Duniya ta tsame kanta daga cikin rikicin.

An sake wallafa wannan sakon a shafukan Facebook na Amharic da na 'yan Tigray.

Sai dai bincikenmu bai gano bayanan mutumin ba, sannan Majalisar Dinkin Duniya ta shaida mana cewa ba ta da bayanai ko sunansa a cikin tsofaffin ma'aikatan da suka yi aiki akalla shekaru 10 da suka wuce.

Hoton da aka yi amfani shi iri daya ne da wanda jaridar Financial Times ta yi amfani da shi a lokacin wani bincike a bara, kan yadda ake amfani da fasahar intanet wajen kirkirar fuskokin mutanen da ba a san da su ba.

Wannan daya ne daga cikin misalan da rahoton kamfanin fasaha na generative adversarial (GANs) ya bayyana.

Mun kuma gano yadda aka goge wani sako da aka wallafa a kasan ainahin sakon na Boton, cikin kasa da mako guda, an kuma yi ta sauya hoton da ke shafin.

A wani lokacin kuma, shafin Twitter din na dauke da hoton babban magatakardar Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres - amma duk da hakan sunan bai sauya daga @GboltonUN.

Amma kwanaki kadan sai aka sauya hoton da na wani mutum, amma sunan bai sauya ba.

Hoton karya na wata majami'a da aka lalata

Tashin hankalin yankin Tigray ya janyo lalacewar gine-gine ciki har da majami'u.

Sai dai wani hoton da aka yi ta yadawa a shafukan sada zumunta na wasu mata biyu da suke addua'a a kusa da wani gini da aka lalata an yi ikirarin wata majami'a ce da aka lalata a Tigray.

Sam hoton ba a Tigray aka dauke shi ba.

Binciken da aka yi kan hoton ya nuna tun a watan Julin 2018 aka wallafa shia shafin Facebook, aka sauya kwanan watan da shekara, a wani shafin intanet na tafiye-tafiye, ya nuna wajen a garin Adi Keih ne na kasar Eritrea.

Shekarar 1999 wato shekaru 20 da suka wuce harin bam da sojojin Habasha suka kai a Eritrea shi ne ya lalata wannan majami'ar. Mun gano ainahin hotunan da aka dauka bayan kai harin da ya lalata ginin ya kuma zo daidai da wanda aka alakanta da rikicin Tigray.

Hotunan yaran nan da ke jin kishir ruwa ba a Tigray ba ne

An wallafa hoto a shafin intanet, da ya nuna yara biyu sun kafa baki suna shan ruwa maras kyau da ke gudana a titi, da ke nuna halin kunci da tashin hankalin da mazauna yankin Tigray ke ciki.

Wanda aka wallafa a Twitter, hade da maudu'in goyon baya ga yankin Tigray , "kadan daga halin matsananciyar yunwar da ake ciki a Tigray."

Sai dai hoton baki daya ba a Tigray ba ne, an dauke shi ne daga yankin kudu maso gabashin kasar Habasha inda masu magana da harshen Somalia suke zaune.

Mun gano hoton da wani mai suna Sayid Abdirahman ya wallafa shafinsa na Facebook, wanda ya shaida wa BBC ya dauki hoton ne a kauyen Awil da ke kudancin kasar a watan Disambar bara.

Mista Abdirahman ya na yawan wallafa batutuwan da suka shafi ruwa da tsafta a yankin da 'yan Somalia da ke kasar Habasha.

Binciken Amurka da bai faru ba

A watan Fabrairu, kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International ta wallafa rahoton cin zarafin dan adam da ta ce sojojin kasashen Habasha da Eritrea sun aikata ta hanyar kai hare-hare muhimman wuraren tarihi da ke garin Axum na Tigray a watan Nuwambar 2020.

Gwamnatin Habasha ta yi watsi da zarge-zargen tare da cewa kirkirarru ne.

Jaridar Herald da ke marawa gwamnatin Habasha baya, ta wallafa ikirarin cewa tawagar hukumar ci gaban kasashen waje ta Amurka USAID ta kai ziyara Axum, amma ba ta gano ko kabari guda da aka binne wani da ya rasu ba ko jin ta bakin iyalan da rahotanni suka ambato an yi wa danginsu kisan kare dangi.

Sai dai USAID ta ce ba ta aike da wata tawagar masu bincike garin Axum ba.

"USAID ba ta gudanar da bincike, ko tura wata tawagar da za ta yi bincike kan abin da ya faru a Axum ba," in ji wata sanarwa da suka wallafa a shafinsu na Twitter.

Source: BBC