Menu

Ronaldo zai tafi Newcastle, Chelsea na gwajin Badiashile, Arsenal na fafutuka kan Mudryk

40309604 Cristiano Ronaldo

Tue, 3 Jan 2023 Source: BBC

Cristiano Ronaldo yana da damar neman tafiya Newcastle United aro, kamar yadda yarjejeniyar kwantiraginsa da Al Nassr ta tanada, idan har kungiyar ta Premier ta samu gurbin buga gasar Zakarun Turai a bana. (Marca)

Babban dan bayan Faransa na Benoit Badiashile, mai shekara 21, ya sauka a London domin gwajin lafiyarsa bayan da Chelsea ta yarda ta saye shi a kan yuro miliyan 38 daga Monaco. (Football London)

Liverpool are na duba yuwuwar sayen dan wasan tsakiya na Portugal Matheus Nunes, daga Wolves a bazara. (Telegraph)

Matashin dan wasan tsakiya na Ingila Jude Bellingham, mai sheakara 19, na shirin ganawa da jami’an Borussia Dortmund kafin ranar 6 ga watan Janairu, inda a lokacin zai gaya musu aniyarsa ta barin kungiyar a bana. Kungiyar ta Jamus za ta bukaci yuro miliyan 100 da sauran tsarabe-tsarabe da za su sa farashinsa ya kai  kusan yuro miliyan 140. (AS)

Atletico Madrid ta tuntubi Arsenal da Manchester United da kuma Chelsea kan bukatar karbar aron dan gabanta na Portugal Joao Felix, mai shekara 23, to amma kuma kungiyar ta Sifaniya na bukatar wadda take sonsa ta biya yuro miliyan 15 da kuma karin yuro miliyan 6 na biyan albashinsa. (Athletic)

Arsenal ta gabatar da tayi na biyu a kan dan wasan Ukraine Mykhailo Mudryk, amma kuma ana ganin farashin ku kusa bai kai abin da Shakhtar Donetsk ke bukata ba yuro miliyan 100. (ESPN)

Manchester United da Bayern Munich na sha’awar Randal Kolo Muani amma kuma Eintracht Frankfurt na neman yuro miliyan 60 zuwa 70 a kan dan wasan na gaba dan Faransa mai shekara 24. (Nicolo Schira)

Manchester City na kokarin ganin ta yi nasarar saye matashin dan wasan tsakiya na Argentine Maximo Perrone, mai shekara 19, daga Velez Sarsfield. (90min)

Newcastle United kuwa za ta ci gaba da tattaunawa ne da Flamengo a kan cinikin matashin dan wasan tsakiya na Brazil Matheus Franca mai shekara 18. (90min)

Kociyan Brighton Roberto de Zerbi na fatan ganin dan wasan tsakiya na Argentina Alexis Mac Allister, ya ci gaba da zama a kungiyar akalla har zuwa karshen kaka. (The Argus)

Arsenal za ta kara tsawon kwantiragin Bukayo Saka na Ingila da kuma William Saliba, na Faransa da shekara daya kowannensu yayin da take tattaunawa da su kan kulla yarjejeniya ta tsawon lokaci da su. (ESPN)

Nottingham Forest za ta bar dan gaban Najeriya Emmanuel Dennis, ya bar kungiyar bayan wata biyar da ta saye shi daga Watford a cinikin da ya kai fam miliyan 10. (Athletic)

Barcelona da Al Nassr sun nuna sha’awarsu ta sayen N'Golo Kante, to amma dan wasan tsakiyar na Faransa mai shekara 31 zai iya sabunta kwantiraginsa da Chelsea. (Fabrizio Romano)

Juventus da Borussia Dortmund sun bi layin zawarcin  matashin dan wasan baya na Sifaniya Ivan Fresneda mai shekara 18 bayan da Newcastle ta fara tuntubar kungiyarsa Real Valladolid. (Fabrizio Romano)

Memphis Depay, zai bar Barcelona, a matsayin wand ba wani kwantiragi a kansa a bazara, maimakon ya neni tafiya a watan Janairu. (Sport)

Source: BBC