BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Shari'un da suka dabaibaye Donald Trump

71148901Donald Trump

Mon, 24 Oct 2022 Source: BBC

Kalubalen shari'un da ke gaban Donald Trump suna da girma kuma iri daban-daban ne. Tsohon shugaban na fuskantar bincike kusan ta kowa ne fanni, kama daga abin da ya shafi takardun sirri na gwamnati da kuma darajar kudin gidansa na New York, da kuma wasu shari'un da yake fuskanta daban-daban. To amma a duk wadannan akwai shari'u manya guda hudu da suke da tasiri sosai a kan shi kansa Trump da kuma siyasarsa. Dukkanin shari'un na gudana kuma zuwa yanzu ba su kai ga tuhumar tsohon shugaban da miyagun laifuka ba. MAR-A-LAGO Ma'aikatar shari'a ta Amurka tana binciken dalilin da ya sa aka kwashe takardun sirri na gwamnati daga Fadar Gwamnati (White House) aka kai su gidan Trump din na shakatawa da ke Florida, Mar-a-Lago, bayan ya sauka daga gwamnati. Yanzu ana gudanar da bincike a kan yadda wadannan takardu suka fita daga fadar gwamnati zuwa gidan na Trump, kuma wwane ne da wa suka samu ganin takardun. A watan Agusta ne aka gudanar da bincike a katafaren gidan na alfarma, kuma an kwace takardu har 11,000 wadanda suka hada da wasu takardun na sirri guda 100. Wasu daga cikin takardun an rubuta cewa takardu ne na manyan sirri. Zuwa yanzu dai ba mu da wani cikakken bayani game da abubuwan da ke cikin wadannan takardu. Abin da yake a fili dai shi ne irein wadannan takardu galibi suna dauke ne da bayanai na sirri na gwamnati wadanda suke da hadari a ce jama'a sun sansu. Me Trump ya ce a kan wannan? Trump ya musanta yin wani abu da ya saba doka, tare da sukar ma'aikatar shari'a a kan binciken da cea bi-ta-da-kullin siyasa ne ake masa. Ya rika gabatar da dalilai na neman kare kansa daga wannan laifi, inda yawanci yake cewa ai ya fitar da takardun daga rukunin na sirri. Sai dai har yanzu babu wata sheda da ya bayar cewa gaskiya ne, ya yi hakan. Yanzu dai wani lauya mai zaman kansa yana duba wadannan takardu na sirri idan har maganganun da Trump yake yi gaskiya ne. Sai dai har yanzu Mista Trump bai amsa ainahin babbar tambayr da ake yi a kan lamarin ba, shi ne cewa tun da farko ma me ya kai takardun gidan nasa. Yaya girman laifin yake? Wannan babban laifi ne da zai iya kaiwa ga tuhuma a gaban shari'a. Daga cikin laifukan da ake ganin Trump ya aikata a kan wannan abu da ya yi, ma'aikatar shari'ar na ganin ya iya saba dokar leken asiri ta kasar, ta hanyar ajiye sirrin tsaro na kasa a gidansa, wanda jhakan zai iya jefa kasar cikin hadari. Baya ga tuhuma a kan takardun sirrin kansu, masu gabatar da kara na kuma duba yuwuwar yi wa shari'a tarnaki na hana ta ta gudana, a matsayin wani babban laifi shi ma. Yanzu dai lauyoyin Trump sun kicime da ma'aikatar shari'a ta Amurkar a kan binciken. Kamfanin Trump na New York : Me ake bincike? Masu gabatar da kara na gudanar da bincike a kan kamfanin iyalan Trump. Akwai bincike biyu da ake yi a nan daya na babban laifi daya kuma ba na wani babban laifi ba ne. Babbar lauyar JIhar New York, Letitia James, tanna jagorantar daya binciken wanda bai shafi babban laifi ba. A binciken wanda ta shafe kusan shekara uku, tana duba yuwuwar ko kamfanin ya aikata abubuwa na zamba a tsawon shekaru da dama a jihar. Binciken ya hada da zargin kara gishiri a darajar rukunin gidajen kamfanin, wanda suka hada da filin wasan kwallon lambu (golf) da otal-otal, domin su samu bashin kudin da suke so da kuma batun haraji. Shi kuma binciken manyan laifukan wanda ya dauki shekaru shi ma babban lauyan lardin Manhattan ne, Alvin Bragg ke jagorantarsa, inda shi ma dai wannan batu yake dubawa wanda ya shafi kamfanin iyalan tsohon shugaban a birnin New York. Me Trump ya ce? Tsohon shugaban da lauyoyinsa sun yi tsayin daka cewa ba wani abu da kamfanin ya yi wanda ya saba doka. Ya zargi Ms James, 'yar jam'iyyar Democrat, da kokarin ramuwar gayya ta siyasa, inda ya bayar da misalin kalaman da ta yi kafin a zabe ta a matsayin babbar lauyar birnin New York. A shedar ya ce ta lashi takobin gurfanar da shi a gaban shari'a inda ta ce shi haramtaccen shugaban kasa ne. Lokacin da aka gayyaci Mista Trump ya bayar da bahasi a binciken wanda bai shafi babban laifi ba, da ya je ya gabatar da sunansa ne kawai, daga nan kuma sai ya yi gum, ya ki cewa uffan. Yaya girman laifin yake? A watan Satumba ne Ms James ta shigar da shari'ar da idan har laifi ya tabbata to kamfanin na iyalan Trump (Trump Organization) za a soke shi daga yanda yake a yanzu, amma a rubuce. Ms James ta ce tsohon shugaban da manyan 'ya'yansa uku da kuma wasu manyan jami'an kamfanin sun tafka laifukan zamba da yawa a tsakanin shekarun 2011 da 2021. A shari'ar ta yi zargin cewa iyalan sun zuzuta darajar kamfanin nasu da biliyoyin dala, a don haka take neman su dawo da dala miliyan 250 da ta ce sun karba ta hanyar zamba. Haka kuma tana neman kotu ta haramta wa Trump da 'ya'yansa rike duk wani matsayi na shugabancin kasuwanci a New York. Ita kuwa tuhumar ta zargin aikata mugun laifi an dan yi shiru da ita zuwa yanzu. To amma duk da haka Babbar Lauyar ta New York ta mika abubuwan da ta gano a binciken ga masu gabatar da kara na tarayya, wanda hakan zai iya kaiwa ga bude wani sabon bincike kan aikata miyagun laifuka. Kutsen Majalisa : Me ake bincike? Hukumomin gwamnatin tarayya da dama suna gudanar da bincike kan irin rawar da ake zargin Mista Trump ya taka kutse da rikicin damagoya bayansa suka tayar a ginin Majalisar Dokokin Amurkar ranar 6 ga watan Janairu na 2021. Masu tarzomar sun yi kokarin hana tabbatar da nasarar da Joe Biden ya samu ne a zabe, ta kayar da Trump. Binciken da aka fi gani zuwa yanzu a kai shi ne na kwamitin majalisa da ke duba irin abubuwan da Trump ya yi a lokacin. 'Yan kwamitin suna zaman jin bahasi wanda ake nuna wa a talabijin, inda ake zargin cewa ikirarin da Trump ya yi na cewa an yi magudi a zaben shi ne ya tunzura magoya bayansa suka yi kutsen tare da tayar da hankali a majalisar. Sakamakon bahasin da suka saurara 'yan kwamitin sun mika takardar gayyata ta hukuma ga Trump ya gurfana a gabansu ya yi bayani tare da gabatar da takardun sheda. Ita ma ma'aikatar shari'a tana gudanar da nata binciken a kan wannan kutse, inda 'yan sanda ke gabatar da binciken da shi ne mafi girma a tarihin Amurka kan lamarin. Me Trump ya ce a kai? Ya musanta hannu a tarzomar tare da sukar kwamitin majalisar, inda ya bayyana kwamitin a matsayin kotun je-ka-na-yi-ka. Ya ci gaba da ikirarinsa na zargin aikata magudi a zaben, abin da har yanzu bai gabatar da wata kwakkwarar sheda ba. Ya girman laifin yake? Kwamitin majalisar wanda ya kunshi 'yan jam'iyyar Democrat 7 da 'yan REpublican 2 ba shi da ikon hukunta Mista Trump, amma tsohon shugaban ka iya gurfana gaban shari'a idan ya ki amsa gayyatar kwamitin. Wanda hakan ke nufin za a iya gurfanar da Trump tare da tuhumarsa da aikata babban laifi. Kuma a nan akwai misalin da ya yi kama da wannan, inda aka yi wa dadadden aminin Trump din Steve Bannon hukuncin daurin gidan yari kan laifin kin amsa gayyatar 'yan kwamitin na majalisa, a ranar da aka aika wa Trump takardar tasa gayyatar. Sai dai a nasa bangaren lamarin da zai kai ga tuhuma da kuma daure tsohon shugaba a irin wannan lamari, abu ne mai sarkakiyar gaske. Tuni binciken ma'aikatar sharia ya kai ga tuhuma tare da daure wasu daga cikin wadanda suka tayar da hankali a majalisar. Neman sauya sakamakon zaben GeorgiaMasu gabatar da kara a jihar suna gudanar da bincike kan zargin kokarin sauya sakamakon zaben shugaban kasa na 2020. An fara gudanar da binciken aikata babban laifi bayan da ta bayyana cewa tsohon shugaban kasar ya yi waya ta tsawon sa'a daya da babban jami'in zabe na jihar a ranar 2 ga watan Janairu na 2021. ''Kawai ina son in samu kuri'u 11,780 ne,'' Mista Trump ya ce a lokacin wayar da ya yi da Ministan Harkokin Waje Brad Raffensperger, dan jam'iyyar Republican. Wadannan kuri'u su ne yake bukata a lokacin ya samu nasara a jihar. Me Trump ya ce? Kamar dai sauran binciken Mista Trump ya bayyana wannan ma a matsayin bi-ta-da-kullin siyasa. Kuma ya soki mai gabatar da kara da ke jagorantar binciken, Fani Willis, a matsayin matashiya mai cike da buri kuma mai tsattsauran ra'ayi 'yar Democrat, wadda ya ce tana shugabantar daya daga cikin wuraren da suka yi kaurin suna da miyagun laifuka da rashawa. Yaya girman laifin yake? "Zargin na da girma sosai. Idan har laifi ya tabbata, ana yanke wa mutane hukuncin zaman gidan yari," in ji Ms Willis a hirarta da jaridar Washington Post a watan da ya gabata. Sai dai ta ce ba lalle ba ne a kai ga tuhuma yanzu, amma ta ce kila nan gaba kadan za a iya gayyatar Mista Trump ya bayar da bahasi. Ba a dai san ko binciken da ake gudanarwa yanzu ya shafi Trump kai tsaye ba, amma dai wasu daga cikin makusantansa na daga cikin wadanda ake bincika. Wani daga cikin wadanda binciken zai hara shi ne tsohon lauyansa Rudy Giuliani, wanda ya jagoranci batun shari'ar kin amincewa da sakamakon zaben. Lauyoyin Mista Giuliani sun ce ba wani abu da ya yi da ya saba wa doka a jihar. Sai dai kafin abin ya kai ga kotu ta kama mutum da laifi, akwai bukatar masu gabatar da kara sun gamsar da kotu da shedu na yankan-shakku cewa wadanda aka tuhuma sun san cewa abubuwan da suka yi magudi ne.

Source: BBC