Menu

Sunak na iya maye gurbin Truss a matsayin sabon Firaiministan Birtaniya

94789313 Rishi Sunak da Boris Johnson

Mon, 24 Oct 2022 Source: BBC

Tsohon ministan kudin Birtaniya, Rishi Sunak ne kan gaba a yunkurin zama sabon Firaiministan Birtaniya, bayan da Boris Johnson ya janye daga kokarinsa na koma wa kan kujerar. A yanzu Penny Mardaunt ce kadai ta rage a cikin masu hamayya da Sunak a takarar shugabancin jam’iyyar Conservative. Tsohon Firaiminista, Boris Johnson ya janye daga takarar duk da cewa ya ce ya samu adadin 'yan majalisar da za su mara masa baya domin shiga takarar sake neman kujerar da ya bari a makonni da suka wuce. Tun bayan da Liz Truss ta yi murabus kwanaki 45 da hawa kujerar Firaiminista a kasar, shi ne aka soma yunkuri na maye gurbinta. Abin da ke nufi kasar za ta samu shugaba na uku a cikin wannan shekarar. Truss ta kasance shugabar da tafi kowa rashin dadewa a kan mulki a tarihin kasar kuma wanda zai maye gurbinsa zai kasance shugaban jam'iyyar Conservative na biyar a cikin shekaru shida. Manyan 'yan takara biyu da za su iya fafatawa su ne Rishi Sunak da kuma Penny Mardaunt. Rishi Sunak Tsohon ministan kudi wanda ya sha kaye a takarar shugabancin jam'iyyar Conservative a watan da ya wuce a yanzu shi ne kan gaba. Iyayen Mista Sunak sun koma Birtaniya ne daga gabashin Afrika kuma asalinsu Indiyawa ne. An haife shi a Southampton, kuma Sunak ya yi karatu a makarantar kudi kafin daga bisani ya shiga jami'ar Oxford da kuma Stanford a Amurka. An zabe shi a matsayin dan majalisar dokoki a Birtaniya a shekarar 2015 sannan kuma a watan Fabarairun 2020 a nada shi ministan kudi. Penny Mordaunt Ta tsaya takarar shugabancin jam'iyyar Conservative a wancen karon amma Sunak da Truss sun shiga gabanta a zagayen karshe. Daga bisani ta goyi bayan Truss, inda aka nada ta a matsayin shugabar masu rinjaye a majalisar dokokin kasar. A shekarar 2019, Ms Mordaunt ta kafa tarihi a matsayin mace ta farko da ta hau kujerar ministar tsaron Birtaniya. Yadda ake zaban sabon shugaba Da farko dan takara na bukatar ‘yan majalisa akalla 100 daga cikin ‘yan majalisa 357 na jam’iyyar Conservative su goyi bayanshi. Hakan na nufin cewa mutum biyu ne kadai za su iya shiga takarar. Idan har mutum daya ne kacal ya samu wannan adadin, to shi zai zama sabon firaiminista ba tare da hammaya ba.

Source: BBC