Batun shugabancin majalisa ta goma na ci gaba da jan hankula da kuma haifar da turka-turka tsakanin 'ya'yan jam’iyya mai mulki a Najeriya har ma da 'yan adawa.
A wannan lokaci ƴan majalisar wakilai masu jiran gado musamman na jam'iyyar APC ne suka ce ba sa goyon bayan da matsayin uwar jam'iyyar ta ɗauka na bayar da sunan waɗanda take so su kasanvce shugaban majalisar da mataimakinsa.
'Yan majalisar ƙarƙashin wata ƙungiya da suka kira 'New Vision 10th Assembly' wadda ta ƙunshi sababbin 'yan majalisa daga dukkan jam'iyyu sun ce zaman majalisar lafiya shi ne, a bar 'yan majalisa da kansu, su zaɓi wadanda suke so su shugabance su.
A farkon makon nan ne, jam'iyyar APC ta fitar da sunan Hon Tajuddeen Abbas daga jihar Kaduna da kuma Hon. Benjamin Kalu daga Abia a matsayin waɗanda zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu da sauran masu ruwa da tsaki a jam'iyyar ke goyon bayan a zaɓe su matsayin shugaba da mataimakinsa.
Zaɓaɓɓen ɗan majalisar ya ce su 'ya'yan jam’iyyar APC da suke shiga majalisa a karon farko, ba za su lamunci kawai a yanke musu hukunci ba tare da bin tsari ba, bisa tanadi na kundin tsarin mulkin kasa.
'Gudun matsala'
Isma'il Dabo, ya ce idan yau arewacin Najeriya aka ce za ta fitar da shugaban majalisar wakilai, sai a bar 'yan majalisa su yanke shawara amma ba wai wasu mutane na daban su yanke hukunci ba.
Ya ce "idan har aka bari wai shugabanci majalisa ba za a bar mutane su yi zaɓensu ba, to matsala za a samu domin majalisar ba za ta yi aikin da ya kamata ba".
Zaɓaɓɓen ɗan majalisar ya ce doka ta ba su damar amfani da cancanta wajen zaɓin mutumin da su 'yan majalisa suka gamsu, ba wai a tilasta musu bin ra'ayin wani ba.
"Amma babban kuskure da za a samu shi ne, a ce wai shugabancin majalisa wasu ne daban za su naɗa kuma su yi tunanin dole kowa ya yi mubaya'a."
"Wasu mutane kalilan ba su da hurumin naɗa shuganacin jam'iyya da kuma juya akalarsa bisa raɗin kansu da abubuwan da suke so".
Hon Ismail ya ce muddin aka aminta da wannan tsari har ya tafi a haka to majalisa ba za ta yi wa kowane ɓangare daɗi ba, kama daga ayyukanta har zuwa ɓangaren zartarwa, babu wanda zai ji dadinta.
Ya ce "dokar kasa ta ce mu yi zaɓe mu zaɓi wanda zai yi jagoranci na adalci domin ci gaban kasa".
"Ba wai muna wannan kumfar-bakin ba ne saboda muna da wata niyya, manufa ko mutumin da mu ke so," in ji Isma'il Dabo.
"Kawai batu ne na dokar kasa, ganin cewa an zaɓo mu ne domin mu yi wakilci , kuma hakki ne a ba mu damar zaɓin wanda zai jagorance mu domin ciyar da Najeriya gaba".
Sharhi
Wannan taƙaddama ta shugabanci majalisa ta 10, ba wai a ɓangaren Majalisar Wakilai kawai ake fama da shi ba, har a Majalisar dattijai akwai waɗanda suke nuna adawa da matsayin da uwar jam'iyyar APC ta ƙasa ke fatan ganin 'ya'yanta sun bi.
Sabbin sanatoci na ganin bai kamata jam'iyyar ta raba shugabancin majalisar da ba a kai ga ƙaddamar da ita ba, bisa dalilai na yawan ƙuri'un da kowanne yanki ya bayar wajen samun nasarar zaɓaɓɓen shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu.
Masu neman shugabancin majalisun tarayya sun fito ne daga ɓangarorin Najeriya na kudu da arewa, kuma akwai wakilcin manyan addinai guda biyu da ƙasar take martabawa.
Sai dai kuma ita Jam'iyyar APC ta yanke shawarar keɓe shugabanci majalisar dattawa ga shiyyar kudu maso kudancin kasar, sannan mataimaki daga ɓangaren arewa maso yamma.
Shugabancin Majalisar Wakilai, an keɓewa arewa maso yamma, mataimakinsa kuma daga arewa maso tsakiyar Najeriya.
Jam'iyyar APC dai bayan wani taro da ta gudanar Laraba, ta ce tana nan a kan matsayinta game da raba muƙamai na shugabancin majalisa ta goma, duk da ƙorafe-ƙorafen da 'ya'yan jama'iyyar suka shigar gabanta.
Ta ce za ta ci gaba da sa ido da kuma ƙorafe-ƙorafe idan akwai.
Ita dai ƙungiyar sabbin 'yan majalisar wakilai mai suna 'New Vision 10th Assembly' tana da mambobi fiye da 240.
Shugabannin ƙungiyar sun ce sun kafa ta ne don ganin ba a yi wa sabbin 'yan majalisa wata dabara a ayyukansu ba.
Yanzu abin zura ido a gani, shi ne yadda wannan dambarwa za ta wanye, kuma ko akwai yiwuwar 'yan majalisun tarayyar za su bi ra'ayin jam'iyyar APC wajen zaɓen sabbin shugabannin da za su ja ragamarsu a majalisa ta goma ko kuma a'a.