BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Sabon rikicin PDP barazana ce ga makomar jam’iyyar — Masana

97277729 Masanan sun yi gargadin cewa rikicin na iya rage tasirin PDP

Wed, 29 Mar 2023 Source: BBC

Wasu masana siyasa a Najeriya, na cewa sabon rikicin da babbar jam`iyyar hamayya a kasar, PDP ta shiga barazana ce ga makoma ko wanzuwarta.

Masanan sun yi gargadin cewa rikicin ka iya rage tasirin jam`iyyar idan jiga-jiganta ba su gaggauta daukar matakan sasantawa ba.

Masanan sun ce da wuya PDPn ta jure wa manyan kalubale biyu da take fuskanta.

Farko, na takaicin rashin gwamnati a matakin tarayya na tsawon shekaru.

Sannan kuma ga sukan da wasu `ya`yanta ke mata, sakamakon rashin jituwar da suka samu da jam`iyyar cewa ta saba wa tsarin karba-karba yayin tsayar da dan takarar shugaban kasa.

Farfesa Kamilu Sani Fagge, malami a jami`ar Bayero ta Kano, ya shaida wa BBC cewa, gaskiya babbar barazana ce ga jam’iyyar PDP, muddin ba ta shawo kan wadannan matsaloli ba, to zai wuya ta farfado ko ta yi tasiri kamar yadda ta yi a baya.

Ya ce, “ mafitar jami’iyyar ta PDP, ita ce ta koma wa wannan tsari na kama-kama, sannan kuma dole sai jam’iyyar ta tsaya ta yi dimokuradiyya ta cikin gida.”

Farfesan ya ce, dole ne kuma sai jam’iyyar ta gina abin da ake kira da’ar jam’iyyar, ma’ana a karfafa ta, ta yadda za ta fi karfin duk wani dan jam’iyyar.

Malamin jami’ar ya ce, “ Muddin za a samu wasu masu hannu da shuni ko masu karfi da za su rinka juya akalar jam’iyyar, to gaskiya za ta sha wuya, sannan kuma ba za ta iya wani tasiri ba, musamman idan ta ci gaba da zama a matsayin jam’iyyar hamayya.”

Rikici na baya-bayan nan da jam’iyyar ta shiga shi ne rikicin da ya biyo bayan babban zabe da ya yi sanadin gurfanar da shugaban jam`iyyar na kasa, Sanata Iyorchia Ayu, gaban kuliya har kotu ta tilasta masa sauka daga mukaminsa.

Jam`iyyar PDP dai ta ga juyi da yawa idan ana maganar rikicin cikin gida da matsalar shugabanci.

Wannan ne ya sa fiye da kashi casa`in cikin dari na mutanen da suka riki kujerar shugabantarta babu wanda ya kammala wa`adinsa cikin girma da arziki.

Amma duk da haka jam`iyyar ta ci gaba da rarrafawa.

A makon nan ne shugaban jam`iyyar PDP na kasa, Sanata Iyorchia Ayu, ya sauka daga mukaminsa bayan wata babbar kotu a jihar Binuwai ta umurce shi ya daina daukar kansa a matsayin shugabanta, sakamakon karar da wasu suka shigar cewa ba shi da hurumin rike mukamin tun da gundumarsa ta kore shi daga PDP.

Source: BBC