BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Sabuwar ƙungiya ta ɓulla a Majalisar Dokokin Najeriya

Majalisar dokokin Najeriya a Abuja

Mon, 8 May 2023 Source: BBC

Wata sabuwar kungiya ta sababbin 'yan majalisar wakilai ta bulla a cikin majalisar dokokin Najeriya.

Wannan na zuwa ne a yayin da ake dambarwa kan shugabancin majalisar ta goma da za a kafa a karshen watan Mayun wannan shekara ta 2023.

Kungiyar da ke kiran kanta 'New Vision 10th Assembly' tana da mambobi fiye da 240.

Shugabannin kungiyar sun ce sun kafa ta ne don hana a yi wa sabbin 'yan majalisa wata dabara a ayyukansu.

Kakakin kungiyar ta 'New Vision 10th Assembly' Bashir Usman Gorau ya yi zargin cewa ana nuna wa sababbin 'yan majalisa wariya a majalisar dokokin Najeriyar don haka ne ya sa suka ga bukatar kafa kungiyar ta sabbin 'yan majalisa zalla.

Gorau ya fada wa BBC cewa duk da bambancin jam'iyyu da ke tsakanin 'yan majalisar, kansu a hade yake.

"Akwai abin da tsofaffin 'yan majalisa ke yi, idan wani abu ya taso suna fara kasa wa kansu ne kafun su waiwayi kanana da ke bayansu, amma mu ba wannan ne ya dame mu ba; Abin da ya dame mu shi ne idan mun yi magana a majalisa za a lura da maganarmu sannan a dauke ta da muhimmanci" in ji Gorau.

Kuma ya yi zargin cewa a wasu lokuta idan sabon dan majalisa ya daga hannu zai bayyana ra'ayinsa kan wani batu sai a ce sai tsohon dan majalisa ya fara gabatar da nashi ra'ayin kafin sabo ya gabatar.

Sabon dan majalisar ya kara da cewa suna bukatar ganin shugabancin majalisa da zai rungumi kowa da kowa ba tare da la'akari da mutum sabo ne ko tsoho ba.

Da aka tambaye shi ko suna yunkurin goya baya ga wani dan takarar shugabancin majalisar ne daga cikin masu nema su jagorance ta, sai ya ce "sun tsaya domin su fahimci wanene daga cikin masu takarar ya fahimci alkibilarsu sannan su mara masa baya."

Source: BBC