BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Sadio Mane ya buga wa Senegal wasa na 100

73264398 Sadio Mane

Sun, 19 Nov 2023 Source: BBC

Tawagar Senegal ta fara wasan neman shiga gasar kofin duniya da kafar dama, bayan da ta doke South Sudan 4-0 ranar Asabar.

Senegal, mai riƙe da kofin Afirka ta fara nasara cin kwallo a wasan farko a rukuni na biyu ta hannun Pape Matar.

Sadio Mane ne ya zura ta biyu a raga a wasa na 100 da ya buga wa tawagar Senegal tamaula.

Matashin ɗan wasa mai shekara 19, wanda ya fara yi wa Senegal ƙwallo, Lamine Camara shi ne ya ci na uku, sannan Mane ya zura na huɗu a bugun fenariti.

Ranar Talata Senegal za ta buga wasa na biyu a cikin rukuni, inda za ta kece raini da Togo a fafatawar da za su yi a Lome.

Senegal ce ta ɗaya a rukuni na biyu da tazarar rarar ƙwallaye tsakaninta Jamhuriyar Congo, wadda take ta biyu.

A wani wasan da aka buga Tanzaniya ta yi nasara a kan Niger da cin 1-0 a Marrakesh a fafatawar rukuni na biyar.

Source: BBC