Menu

Sallar tarawihi da abubuwan da ke tattare da ita

Hoton alama

Fri, 7 Apr 2023 Source: BBC

Daya daga cikin ibadun da watan Ramadana ya ke tattare da su na musamman shi ne salloli da ake yi a cikinsa da ba a yi a ko wanne wata.

Sallah irin ta tarawihi da ake farawa daga farkon watan zuwa arshe, a wajen wasu malaman kuma zuwa kwana asherin ɗin farko na watan.

Sai kuma sallar tuhajjuj da ake yi a kwana 10 ko taran ƙarshe na watan, wadda ita ma ta musamman ce da ake keɓence watan da ita.

BBC ta yi tattaunawa ta musamman kan abubuwan da suka shafi sallar tarawihi da kuma fa'idojinta.

Malam Muhammad Khaifa Mashhood wani fitacce malamin addini ne a jihar Bauchi, kuma ya yi bayani dalla-dalla kan abubuwan da suka shafi wannan sallah.

Mece ce sallar tarawihi?

A larabace ma'anar tarawihi shi ne hutu, "to ana kiranta sallar hutu ne saboda ana hutawa yayin yin sallar duk bayan raka'a biyu," in ji Malam.

Ya aka yi ta samo asali ?

Ta samo asali ne lokacin Annabi Muhammad, ya ftio ya yi sallar tare da jama'a a dare na farko haka zalika a dare na biyu na watan Ramadan, amma sai aka ga ba a ganshi ba a dare na uku, ko da aka tambaye shi sai ya ce "baya son ya mayar da ita tamkar ta wajibi a wajen al'umma".

Malam ya ce "mai tausayi ne Shi ga al'umarsa shi ya sa yaƙi fita. Lokacin sayyadina Abubakat ba a yi tarawihi a jam'i ba. Amma a lokacin sayyadina Umar an yi ta a jam'i kuma shi ya ɗabbaƙata," in ji Malam.

Raka'a nawa ake yi a tarawihi?

Malam ya ce "Annabi Muhammad ya fara sallar ne da raka'a 10, kuma duk wanda zai yi an fi so ya yi 10 zuwa 20, kar dai ya matsawa kansa.

"Manufar addini cike take da sauƙi, addinin Musulunci ba ya nufin tsaurarawa ko matsawa jama'a," in ji Khalifa Mashhood.

Dole ne sai na yi tarawihi a bayan liman?

Abin da ya kamata a sani shi ne, tarawihi sallar nafila ce ba wajibi ba, ko sallar wajibi in ba ka samu cikin jam'i ba sai ka yi a gida.

To ita kuma nafila an fi son a yi ta a gida, domin an umarci mutane su riƙa salla a ɗakunansu kada su mayar da su kamar maƙabartu.

Ya tsarin karatun sallar ya kamata ya zama?

Ba wanda ya ce zai ka yi dogon karatu a cikin wannan sallah.

Idan kai ɗaya ne ko hizifi ɗaya za ka rika karantawa duk raka'a babu wanda zai ce ka yi laifi, ya danganta da lafiyarka.

Na biyu kuma ya danganta da inda mutum ya iya kartun Ƙur'ani, in baka iya ba sosai ka karanta abin da ya samu.

Za ka iya irin yadda ake yi a yankin arewacin Najeriya, "daga Alamtara kaifa zuwa nasi".

Mece ce fa'idar tarawihi?

Fa'idar sallar tarawihi na da dama, saboda hadisi ya tabbata Annabi ya ce "wanda ya tsaya kai da fata tsakanin da Allah ya yi azumin Ramadana za a gafarta masa zunubansa," in ji Malam.

Zan iya katse sallar tarawihi na je wasu ayyukan na dawo?

Kamar yadda na fada a baya, sallar ta nafila ce, yin ta za a samu lada, barin ta kuma ba zai zama laifi ba.

Sai dai a ce mutum zai yi asarar lada mai yawa.

Yaushe ya kamata a fara tarawihi?

Daga lokacin da "shafaqi" ya buya to za a iya fara sallar tarawihi.

Shafaqi shi ne sauran hasken nan na bayan sallar Magariba, ma'ana daga lokacin da za a fara sallar isha'i to daga nan za a fara sallar tarawihi.

Source: BBC