BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Saudiyya na harin Salah, Real Madrid na sa ido a kan 'Messin Turkiyya'

Mohamed Salah

Fri, 23 Jun 2023 Source: BBC

Dan wasan gaba na Liverpool Mohamed Salah, shi ne tauraro na gaba da gasar Saudiyya ke harin janyewa bayan zuwan Karim Benzema da N'Golo Kante. (Four Four Two)

Real Madrid na sa ido a kan matashin dan wasan Fenerbahce Arda Guler, mai shekara 18, wanda ake wa lakabi da Messin Turkiyya. (Mail)

Messi, ya gaya wa Kylian Mbappe, cewa ya kamata ya nemi wata kungiya da zai ci kofuna. (Defensa Central)

Wakilin Jurgen Klopp ya kawar da yuwuwar tafiyar kociyan na Liverpool domin maye gurbin Hansi Flick a matsayin mai horad da tawagar Jamus. (Mirror)

AC Milan na fatan yin galaba a kan manyan abokan hamayyarsu Inter Milan wajen sayen Romelu Lukaku, duk da cewa dan wasan na Belgium ya yi kakar da ta gabata ne a Inter a matsayin aro. (Gazzetta dello Sport )

Manchester United ta cimma matsaya da Chelsea a kan cinikin Mason Mount, inda suke dab da kammala cinikin a kan fam miliyan 60. (Mirror)

Kociyan Arsenal Mikel Arteta na ganin Declan Rice, zai iya kasancewa kyaftin din kungiyar a nan gaba, kuma Gunners din na shirin gabatar da tayi na uku a kan dan wasan na Ingila, wanda kudin zai kusa da farashin da West Ham take bukata. (Mail)

Rice ya fi son ya je Arsenal duk da cewa Manchester City na shirin shiga cinikin ita ma kuma za ta iya biyan fam miliyan 100 da West Ham ta sa a kansa. (Guardian)

Tottenham ta zama kungiyar da ta yi nasara da za ta sayi James Maddison na Leicester City da Ingila. (Guardian)

A shirye Bayern Munich take ta bai wa dan bayan Manchester City da Ingila Kyle Walker, kwantiragin shekara biyu. (Bild )

Fulham ce kan gaba a kungiyoyin da ke zawarcin dan wasan tsakiya na Southampton da Ingila James Ward-Prowse, bayan da Southampton din ta fadi daga Premier. (Independent)

Kociyan Fulham na tunanin amsa goron gayyatar tafiya kungiyar Al-Hilal ta Saudiyya wadda ta yi masa tayin albashi mai tsoka sosai. (i Sport)

Borussia Dortmund na shirin taya matashin dan wasan Manchester United da Tunisia Hannibal Mejbri, mai shekara 20, fam miliyan 13. Ya yi zaman aro ne a kakar da ta gabata a Birmingham. (Manchester Evening News)

Haka kuma kungiyar ta Jamus na sha'awar sayen Cole Palmer na Manchester City a kokarin da take yi na neman wanda zai maye gurbin Jude Bellingham. (Bild )

Kungiyoyin Premier hudu, Brentford, da Fulham, da West Ham da kuma Wolves za su yi gogayya da Sporting Lisbon wajen neman sayen Viktor Gyokeres dan Sweden da aka yi wa kiyasin farashi fam miliyan 25, daga Coventry City. (Mail)

Manchester United ta bai wa kungiyar Jose Mourinho, Roma daman sayen Donny van de Beek, dan Netherlands. (Metro)

A ranar Juma'a za a yi gwajin lafiyar dan wasan Roma din Justin Kluivert, a Bournemouth, kafin a kammala cinikin dan Hollandin a kan yarjejeniyar shekara biyar. (Fabrizio Romano)

Dan wasan tsakiya na Arsenal da Ghana Thomas ya yarda ya tafi Juventus, ya yi watsi da gayyatar da aka yi masa zuwa gasar Saudiyya. (Sky Sports )

Source: BBC