BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Shin Messi zai kara fafatawa da Ronaldo ?

Lionel Messi

Fri, 20 Jan 2023 Source: BBC

A cikin sahara a Saudiyya, Cristiano Ronaldo da Lionel Messi suka hadu a ranar Alhamis domin buga wasan sada zumunci.

Daga karshe an zura kwallo tara a wasan, inda aka tashi Paris St-Germain nada ci biyar ita kuma tawagar Riyadh All-Star nada ci hudu.

Ronaldo ya zura kwallo biyu, shi kuma Messi ya ci kwallo daya.

Wasan na sada zumunci ya hada kan manyan 'yan wasan PSG watau Mbappe da kuma Neymar da Messi a waje daya.

Messi ne ya soma cin kwallo a wasan kuma kafin a tafi hutun rabin lokaci Ronaldo ya ci kwallo biyu.

Bayan awa daya ana gumurzu a wasan, sai aka cire Messi da kuma Ronaldo daga fili suka koma benci.

Sai dai masu sharhi na ganin cewa da kamar wuya manyan 'yan wasan biyu su kara haduwa a fili domin buga wasa.

Source: BBC