0
MenuAfrica
BBC

Shin ko karshen zaman De Gea a United ya yi ne?

Tue, 13 Apr 2021 Source: bbc.com

A ranar Lahadi Manchester United ta je ta doke Tottenham da ci 3-1 a wasan mako na 31 a gasar Premier League da suka fafata.

Sai dai kuma Ole Gunnar Solskjaer ya yi amfanni da Dean Henderson a matakin mai tsaron raga, maimakon David de Gea wanda ya yi zaman benci.

De Gea, golan tawagar Spaniya ya yi wa United wasa 24 daga 31 a gasar Premier League ta bana.

Kuma wannan shi ne karon farko da De Gea zai fuskanci kalubale a gurbin mai tsaron ragar United.

Wannan ne karon farko da Henderson ya tsare ragar babbar kungiyar Manchester United, bayan da ya yi wasannin aro na kaka biyu a Sheffield United.

Henderson mai shekara 24, wanda ya buga wa tawagar Ingila tamaula a watan Nuwamba, an sa ran tun farko shi ne zai maye gurbin De Gea, amma ba a dauka nan kusa ba.

De Gea wanda ya koma United a kakar 2011, ya tsawaita zamansa a Old Trafford zuwa karshen kakar tamaula ta 2023,

Source: bbc.com