BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Shin me ya sa hare-haren 'yan fashin daji ke dawowa a Najeriya?

Hoton alama

Tue, 4 Apr 2023 Source: BBC

Ana ci gaba da nuna fargaba a Najeriya saboda ƙaruwar hare-haren 'yan fashin daji a sassan arewacin ƙasar, kwanaki ƙalilan bayan kammala zaɓuka.

A ranar Lahadi ne, gwamnatin jihar Kogi ta tabbatar da kashe gomman mutane da raba ɗumbin wasu da mutsugunansu a ƙauyen Aloko cikin yankin Dekina, bayan wani harin wasu ‘yan bindiga da ba a tantanace ko su wane ne ba.

Gwamnati ta ce maharan waɗanda yawansu ya kai kusan 100 sun kai hari yankin ne, daga sansaninsu da ke maƙwabtaka.

Harin na zuwa ne daidai lokacin da wasu 'yan bindiga suka sace ɗalibai kusan guda 10 a ƙaramar hukumar Kachia ta jihar Kaduna. An kuma samu irin wannan hari da ya yi sanadin sace ɗalibai mata biyu daga Jami'ar Tarayya ta Gusau a jihar Zamfara mai maƙwabtaka.

A tsakiyar watan Maris ma, 'yan fashin daji sun kashe kusan mutum 21 a wani mummunan hari da suka kai cikin ƙaramar hukumar Ƙanƙara ta jihar Katsina.

Wani artabu tsakanin 'yan fashin daji da jami'an ‘yan-sa-kai bayan wata walima da wani riƙaƙƙen ɗan fashi mai laƙabin Mai-katifar-mutuwa ya yi a ƙauyen Majifa.

Bayanai sun ce bayan tashi daga walimar ne a hanyarsu ta komawa inda suka fito, ‘yan bindigar suka riƙa kai farmaki kan ƙauyukan yankin.

Haka zalika, akwai rahotannin kai hare-haren 'yan fashin daji a sassan ƙasar ciki har da a jihohin Taraba da Neja.

Ana iya lokacin luguden wuta da jerin farmaki da dakarun tsaron Najeriya ke kai wa sansanoni daban-daban na gungun maharan, sun janyo samun lafawar hare-hare, kafin ga alamu su sake dawowa ko kuma samun ƙaruwarsu.

Wani ƙwararre kan harkar tsaro a yankin Sahel, Dr Kabiru Adamu ya ce da ma matakan da aka ɗauka a kan 'yan fashin dajin, matakai ne na ɗan taƙaitaccen lokaci, don haka babu mamaki, idan hare-harensu suka dawo a yanzu.

"Wa'yanda suke kai hare-haren nan, wato ƙungiyoyi wa'yanda suke riƙe da makamai, kusan za mu ce, ba mu magance matsalarsu ba".

Source: BBC