Faransa ta miƙa wuya bayan ta amince da janye dakarunta 1,500 daga Nijar, inda aka shafe watanni, ana jayayyar diflomasiyya tsakanin hukumomin Paris da sojojin da suka yi juyin mulki a watan Yuli.
Shugaba Emmanuel Macron ya ce ya ɗauki matakin ne saboda sojoji masu mulki a Nijar "ba sa son a yi yaƙi da ta'addanci", kuma suna son su ci gaba da garkuwa da Shugaba Mohamed Bazoum, wanda shi ne "halastaccen shugaba".
Ana nuna wa Faransa ƙiyayya mai ƙarfi, tun bayan cire Bazoum.
Masu zanga-zanga sun yi zaman dirshen a sansanin sojin Faransa da kuma ofishin jakadancinta da ke Yamai.
A can gida Faransa, Mista Macron na fuskantar matsin lamba. Majalisar dokokin ƙasar ta tafka muhawara a kan ko akwai buƙatar janye dakarun ƙasar daga Sahel, tun a shekara ta 2020. Hakan ya zo ne bayan abubuwan da suka faru a Mali da Burkina Faso.
Shugabannin da suka yi juyin mulki sun yi amfani da guguwar ƙin jinin Faransa a Nijar, wajen ƙara samun wurin zama.
A Nijar, akwai zargin cewa Shugaba Mohamed Bazoum ɗan koren Faransa ne. Sojojin da suka ƙwaci mulki a ƙarƙashin jagorancin Janar Abdourahmane Tchiani sun soke yarjejeniyoyi biyar da aka ƙulla can shekarun baya da Faransa.
Ƙaruwar ƙin jinin Faransa, ta sa ala tilas dakarun Faransa su fice daga Nijar kamar yadda Bram Posthumus, ƙwararre a kan harkokin Sahel ya bayyana.
"Ba su da wani zaɓi, kuma dole su kare mutuncinsu. Babu makawa. Amma Faransa ta nuna cewa ita ce ta ga damar janye dakarunta, ba wai don abubuwan da sojojin Nijar suka ce ba," in ji Posthumus.
Mutane da dama a Nijar sun fusata da ayyukan Faransa a ƙasar, tun bayan da sojoji suka kifar da gwamnatin dimokraɗiyya.
Sun ce Faransa ta nuna baki biyu game da juyin mulkin da aka yi a Gabon da kuma wanda aka yi a Chadi a shekara ta 2021.
Rashin fitar da matsaya iri ɗaya, shi ne ya ƙara janyowa Faransa baƙin jini, in ji Abdoulaziz Abdoulaye Amadou, wani malamin addini a Yamai.
"Me ya sa Emmanuel Macron yake cewa bai yarda da mulkin soji ba? Bayan ya amince da sojoji a Gabon da Chadi. Abin da ya ba mu haushi ke nan. Faransa ta raina mana wayo," in ji Amadou.
Dakarun Faransa sun je Nijar ne domin yaƙi da masu iƙirarin jihadi a ƙasashen Sahel.
Amma duk da maƙudan kuɗaɗen da ta kashe da kuma aika sojoji masu yawa, Faransa ta gaza wajen hana masu ikirarin jihadi ƙwace yankuna.
"Duk da yake, dakarun Faransa ba su iya hana hare-haren mayaƙa masu iƙirarin jihadi ba, amma dai an samu sauƙi", in ji Bram Posthumus.
A bara, an samu raguwar mace-mace sakamakon ayyukan ta'addanci a Nijar da kashi 79 cikin 100. Ko da yake, babu tabbas idan kasancewar sojojin Faransa ya taimaka wajen samun raguwar, amma dai masu sharhi sun ce rashin mulkin siyasa, ka iya mayar da hannun agogo baya.
A Mali da Burkina Faso, sojojin da ke mulki na ƙoƙarin tabbatar da ikonsu, amma dai ana samu ƙaruwar hare-haren ta'addanci. Akwai fargabar cewa Nijar ma abin zai iya muni.
An samu ƙaruwar hare-hare a Nijar tun bayan da sojoji suka ƙwace mulki musamman a yankin Tillabéri da ke kusa da kan iyaka da Burkina Faso.
Ficewar dakarun Faransa zai iya kawo giɓin da masu ta-da-ƙayar-baya za su yi ƙoƙarin cikewa, in ji Mista Posthumus.
"Abin da kuka gani a Mali shi ne zai faru a Nijar saboda dakarun ba su da ƙarfin kare ɗaukacin ƙasar," in ji shi.
Rashin ƙarfin kare yankunansu, ka iya shafar ayyukan haƙo ma'adanai.
A cikin shekara goma, ƙasar Kazakhstan ce kawai ta fi Nijar shigar da Uranium zuwa Faransa. Ma'adanin da Faransa ke amfani da shi wajen samar da lantarki kashi 70 cikin 100 a ƙasarta.
Kuma akwai fargabar za a iya katse aikin fitar da Uranium din.
Kamfanin Orano wanda a baya ake kiransa Areva, ya ce zai ci gaba da ayyukansa a garin Arlit da ke arewa maso yammacin Nijar duk da irin yanayin da ake ciki a ƙasar.
Wataƙila sojojin da ke mulki za su sake ƙulla yarjejeniya game da haƙo ma'adanin Uranium, in ji Mr Posthumus, kuma bisa dukkan alamu 'yan siyasa ne za su ci riba, ba talakawan ƙasar ba.
Duk da arziƙin man fetur da kuma ma'adanin uranium da Nijar ke da su, amma dai kashi 40 cikin 100 na al'ummarta, miliyan 25 na rayuwa cikin matsanancin talauci.
Ba kamar ƙasashen Mali da Burkina Faso wadanda suka buƙaci ɗaukacin dakarun ƙasashen waje su fice daga ƙasarsu ba, ita kuwa Nijar ba ta nemi dakarun Amurka 1,000 su bar ƙasar ba.
Hakan zai bai wa Nijar ɗin damar ƙulla alaƙa da Rasha kamar yadda Mali da Burkina Faso suka yi.
Masu sharhi sun ce rage ƙarfin faɗa-a-ji na Faransa a Nijar, ba ƙaramin al'amari ba ne musamman a siyasar ƙasar.
A cikin shekaru masu zuwa shugabannin soji a waɗannan ƙasashe za kuma su iya kifar da gwamnatoci, inda za su iya kafa hujja da cewa suna ƙoƙarin rage tasirin Rasha ne a harkokin ƙasashensu.