Duk da cewa ana gane shekaru ne ta hanyar daɗewar mutum a raye, amma masana kimiyya sun ce za su iya yin gwajin da zai nuna yadda gaɓoɓi daban-daban na cikin jikin ɗan'adam ke tsufa.
Hakan zai taimaka wajen hasashen gaɓar da za ta iya fuskantar matsala a gaba.
Tawagar masanan a Jami'ar Stanford sun ce za su iya sanya ido kan manyan gaɓoɓi 11 na jikin ɗan'adam, ciki har da zuciya da ƙwaƙwalwa da kuma huhu.
Masanan sun gwada yin haka a kan dubban mutane masu matsakaitan shekaru da kuma waɗanda suka fara tsufa.
Binciken ya gano cewa kowane mutum ɗaya a cikin mutum biyar masu lafiya, wadanda shekarunsu suka kama daga 50 zuwa sama, kan samu aƙalla gaɓa ɗaya a jikinsa da ke saurin tsufa fiye da saura.
Sannan kuma mutum ɗaya zuwa biyu cikin mutum 100 kan iya samun gaɓoɓi da dama a jikinsu da suka fi sauran jikinsu tsufa idan aka kwatanta da shekarunsu na haihuwa.
Duk da cewa yin irin wannan gwaji zai iya kasancewa mai ban-tsoro, amma wata dama ce ta yin rigakafi game da duk wata matsala da wata gaɓa za ta iya samu a shekaru masu zuwa, kamar yadda masanan suka faɗa.
Sanin gaɓar jiki da ke tsufa fiye da shekarun mutum zai taimaka wajen gano irin rashin lafiyar da mutum zai iya fama da ita a gaba, kamar yadda masanan suka faɗa a wata mujallar bayanai kan halittu.
•Hanji
•Ƙoda
•Kitse
•Jijiyoyi (kafofin tafiyar jini)
•Tsokokin garkuwar jiki
•Tsokar jiki
•Saifa
Gwajin jinin da ake yi a lokacin wannan bincike kan gano yanayin yawan sinadarin proteins domin gano gaɓoɓin da ke tsufa cikin sauri fiye da saura.
Ta hanyar hakan za a iya gane yawan sinadarai daga kowace gaɓa.
Masu bincike sun koyar da na’ura za ta iya hasashen abubuwan da ke faruwa a gabobin ta hanyar bayanai da aka samu daga gwaje-gwajen jini na wanda za a yi wa gwajin.
Daya daga cikin masu binciken, Dr Tony Wyss-Ciray ya ce “Lokacin da muka auna shekarun gabobin mutanen masu lafiya da aka yi binciken a kansu, sai muka gani cewa kashi 18.4% na masu shekara 50 ki fiye suna da akalla gaba daya da take tsufa da sauri fiye da saura.
“Kuma sai muka gano cewa wadannan mutane sun fi shiga cikin hadarin samun wata cuta da za ta shafi wannan gabar a cikin shekara 15 masu zuwa.”
Yanzu haka dai jami’ar Stanford ta kika bayanan da ta hada ga masu hakkin mallakar gwaje-gwajen, kan yiwuwar za a iya amfani da su a nan gaba.
Sai dai ana bukatar kara yin bincike game da batun hasashen shekarun gabobi da lafiyarsu kafin dorawa.
Wasu daga cikin bincike-binciken Dr. Wyss-Ciray sun nuna cewa tsufar gabobi ba tana faruwa ba ne a hankali a hankali, sai dai takan karu ne a tsakankanin wasu lokuta na rayuwa, inda tsufar kan kara sauri lokacin da wasu mutanen suke cikin shekarunsu na 30 ko kuma a farko-farkon shiga shekara 60 ko 70.
Farfesa James Timmons, masani kan alakar cutuka da shekarun mutane a jami’ar Queen Mary da ke birnin Landan shi ma ya yi wasu ayyukan game da yanayin tsufa da jikin dan’adam. Nasa aikin ya mayar da hankali ne kan sauye-sauye da ake iya samu a kwayoyin halittar gado a maimakon lura da sinadaran proteins.
Ya ce abubuwan da Dr Wyss-Coray ya gano a baya-bayan nan sun burge sosai, sai dai ana bukatar kara tabbatar da hakan a tsakanin wasu karin mutanen, musamman mutane masu kananan shekaru daga yankuna daban-daban na duniya.
Dr. Wyss-Coray ya ce “Idan da a ce za mu yi irin wannan gwaji kan mutane 50,000 ko 100,000, hakan na nufin za mu iya ganowa da kare mutane daga kamuwa da rashin lafiya, tun kafin rashin lafiyar ta zo, ta hanyar gano gabobin da ke tsufa cikin sauri a jikin mutum.
sai dai Caroline Abrahams ta kungiyar Age UK ta ce duk da cewar abu ne mai kyau a gani cututtukan da za su iya afkuwa sanadiyyar tsufar gabobi, akwai kuma bukatar a yi la’akari da yadda mutane za su ji idan suka fahimci cewa suna dauke da cutar.
Ta ce idan har za a rungumi wannan al’amari, to kuwa mutane za su bukaci a ba su kulawa ta hanyar shawarwari da magunguna a lokacin sanar da su sakamakon binciken da aka yi a kansu, kuma dole hukumomin kula da lafiya su san da hakan sannan sun shirya masa.