BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Sinadarin da mai yiwuwa ya dakushe armashin Babbar Sallah bana

Hoton alama

Sun, 2 Jul 2023 Source: BBC

Babbar Sallar Layya, babban biki ne a ƙasar Hausa na al'ummar Musulmi da ke zuwa duk shekara.

Dangi da 'yan'uwa masu yawa na amfani da bikin wajen ƙarfafa zumunci da kyautata wa maƙwabta da abokan arziƙi.

Biki ne da akan yanka rago ko sa, ko wata dabba da aka shar'anta a matsayin layya.

Iyalai kan yi tuwon sallah, wasu ma kan yi sabon ɗinki, a saya wa yara takalma da 'yan kunne ga mata.

Dangi kan zo gida bikin sallah har daga garuruwa masu nisa. Wasu ma, kamar ahalinsu Shafi'u Adamu, sukan haɗu a irin wannan lokaci, su hau motoci suna bi gida-gida don gaishe da iyaye da 'yan'uwansu mata da ke aure a sassa daban-daban na birnin Kano.

"Mukan jera mota shida ko takwas har fiye ma. Da mu matasan, da ƙannenmu waɗanda suka taso, da kuma waɗanda suka yi aure."

Daɗaɗɗiyar al'adar ƙarfafa zumunci ce da Shafi'u, ɗan shekara 34 ya taso ya ga ana yi duk lokacin bikin sallah a gidansu.

Ziyara ce, ta barka da an shekara lafiya, wadda kan sada fuskokin gomman dangin da suka shafe tsawon lokaci, ba su ga juna ba.

"Idan muka yi wannan zagayen, to su, ya fi ka ba su kuɗin barka da sallah. A zo ɗin kawai suke buƙata. Su ga 'yan'uwansu sun zo gaba ɗaya, a zauna ana hira," in ji shi.

"A yi hoto. Don duk muna yin hoto, in muka je. In muka dawo, mu yi posting a guruf ɗin gida. Kowa na murna, an je gidan wance, an je gidan wance".

A cewarsa, sukan kusan zagaye birnin da bikin sallah. "Mu je Kurna, mu shiga Hotoro, sannan mu taho Na'ibawa, daga nan mu zo mu shiga Sheka, duk family ne muke zagayawa tsawon wuni a hankali".

Sai dai a bana, man fetur ɗin da motocin kwambar gaisuwar sallah da su Shafi'u ke buƙata, kuɗinsa ya ninninka.

"Bana dai abin gaskiya... Ba zai yiwu ba. Saboda wannan tsadar fetur ɗin".

Sanarwar da sabon shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya bayar ranar 29 ga watan Mayu, ta cire tallafin man fetur a ƙasar, ta yi tasiri cikin ɗumbin al'amuran rayuwar 'yan Najeriya.

Ga alama kuma, ta dakushe armashin bikin babbar sallah ga iyalai masu yawa a bana.

Litar man fetur ɗaya ta kai N540 a gidan mai, maimakon farashin N197 da ake sayarwa watanni kaɗan da suka wuce.

An dai lura da raguwar zirga-zirgar ababen hawa a titunan birane irin Kano tun ma kafin zuwan bikin sallah.

Tituna masu yawan hada-hada a wasu lokutan sukan zama ababen hawan da ke sufuri sai tsilla-tsilla.

Da yawan masu motoci sun jingine ababen hawansu masu shan mai, maimakon haka, sun rungumi babura, masu ƙarancin buƙatar fetur, wasu ma sun koma kekuna.

Hatta motocin haya sun rage zirga-zirga saboda ƙarancin fasinjoji, ga shi kuma ribarsu na ƙara kwararewa wajen sayen fetur mai ɗan karen tsada.

Wani direban babur mai ƙafa uku a birnin Kano ya shaida wa BBC cewa a yanzu ba ya zagaya titi yana ta ɓarin wuta da sunan neman fasinja kamar yadda suke yi a baya.

Ya ce yakan tsaya ne kawai wuri ɗaya a wata mahaɗa ko tashar mota, sai ya samu fasinja sannan ya hau titi.

'Wasu a cikinmu sun ajiye motocinsu'

Shafi'u Adamu ya ce wasu a cikin 'yan'uwansa su ma, sun ajiye motocinsu tun kafin zuwan sallah, abin da ya sanya a wannan karo suka yanke shawarar dakatar da ziyarce-ziyarcen da suka saba yi shekara da shekaru.

Maimakon su hau motoci su je ƙafa-da-ƙafa, in ji shi. Yanzu za su kira dangi da 'yan'uwa ta wayar tarho ne kawai a gaisa.

"Saboda, in wani ya zo, ba a ɗauke shi an zaga da shi ba, to wani ba zai ji daɗi ba".

Matashin ya ce: "Wani a Katsina yake aiki, wani a Jigawa, wani na zuwa ne daga Kaduna.

To, duk gaba ɗaya ake zuwa ranar sallar nan, a haɗu a family house. Sai a shiga motoci. Kai ka shiga motar wancan, wancan ya shiga motar wannan, sannan a ɗunguma a tafi".

A cewarsa, sun yi shawarar ko mota ɗaya ce a bana su zuba man fetur don zuwa gaishe-gaishen sallah, amma dai daga bisani suka haƙiƙance a kan cewa hakan ba mai yiwuwa ba ce.

"Da wa za a je? Shafi'u ya tambaya. "Waye za a ɗauka, waye ba za a ɗauka ba?"

Ya ce a baya har ɗauko ƙarin motar bas ta haya suke yi, saboda albarkar da suke da ita, su ƙara a tafi ziyara.

Matashin ya ce idan ya duba albashinsa, ya ga man fetur ɗin da yake buƙata don zuwa aiki, sai ya ga abin ba mai yiwuwa ba ne don kuwa kuɗin sun zarce cefanen gidansa. "Rayuwar ta fi ƙarfin talaka yanzu," in ji shi.

Mai yiwuwa, dangi da yawa ne suka bi sawunsu Shafi'u a wannan biki, wajen jingine motocinsu, su haƙura da yawon sallah.

Ana iya samun masu ƙarfin hali da ƙila, za su taƙaita ziyarar kamar yadda su Shafi'u ma suka yi tunanin yi.

Sai dai shi ya ce hakan ba abu ne mai yiwuwa ba a gare su. "Farin cikinsu, su ga an je da wannan yawan."

Ya ce 'yan'uwansu da suke kai wa ziyarar sukan alfaharin cewa danginsu sun zo gaishe su, har sukan nuna wa maƙwabta cewa "ga danginmu".

Wani babban ɓangare na bikin sallah wanda mai yiwuwa shi ma zai iya gamuwa da cikas sanadin tsadar man fetur bana, shi ne tafiya wuraren nishaɗi kamar gidan adana namun daji da dandalin wasan yara da kantunan sayar da kayan tanɗe-tanɗe da lashe-lashe.

Tsadar rayuwa da ƙarancin kuɗin shiga sun rage nauyin aljihun mutane da yawa.

Maimakon kai yara zuwa irin waɗannan wurare, waɗanda a bukukuwan sallah na baya, akan ga sun yi cikar kwari, wasu masu bikin sallar za su zaɓi su yi zamansu a gida kawai.

Kwana biyu kafin Babbar Sallah, wasu matafiya da ke kan hanyarsu ta zuwa gida a Abuja, babban birnin ƙasar, sun koka kan yadda tashin farashin man ya haddasa ƙarin kuɗin mota.

Wani fasinja mai suna Muhammad Sani Najeriya ya ce "tsadar kuɗin mota ba za ta hana ni zuwa Kano ganin iyalina ba, ko da yake, ta rage nauyin guzurin da zan tafi da shi".

Ya ce a baya yana biyan N4,000 zuwa Kano, amma yanzu ya koma N9,000.

"Ni yanzu ba a son raina zan biya wannan kuɗin ba, kuma a haka ma don zan tafi kafin jajiberen sallah ne."

Wata fasinjar Bauchi ta ce ba za ta iya biyan N9,000 ba, a madadin haka sai ta haɗa gwiwa da wata suka biya N7,000 kowacce, inda za su zauna su biyu a kujerar gaba.

Ba mu taɓa fashin ziyarar sallah ba

Shafi'u Adamu ya ce bikin sallar bana, ga alama ba zai yi armashi ba. Rashin samun damar kai ziyara ga 'yan'uwa da danginsu a wannan lokaci, "a gaskiya mun ji ba daɗi".

Ya ce tun da ya taso a rayuwarsa, bai taɓa ganin an yi fashin wannan al'ada ta ziyarce-ziyarcen sallah a gidansu ba. "Wallahi ba mu taɓa fashin abin nan ba, tun da nake."

Matashin ya ce a cikin ziyarar sallah da suke zuwa har da yayye da ƙannen mahaifinsa. Dangi ne sosai ake haɗuwa, in ji shi. "Ga 'ya'yan yayyen mahaifinmu da 'ya'yan ƙannensa, saboda duk mun taso gida ɗaya."

Ya ce bayan yanke shawarar cewa ba su yi ziyarar sallah a bana, sun jirkinta faɗa wa dangin da suka saba zuwa gidajensu, sai a ranar sallah.

Shafi'u dai ya yi fatan samun sauƙin rayuwa.

A cewarsa, tun tuni tsadar rayuwar da ake ciki, ta fi ƙarfin albashin ƙaramin ma'aikaci irinsa.

"Ina roƙon gwamnati, ta dubi Allah ta kawo sassauci cikin al'amuran rayuwa ko kuma ta yi ƙarin albashin da zai yi daidai da wannan hali."

Zuwa yanzu dai, ba a ga wani ƙwaƙƙwaran mataki da hukumomin ƙasar suka ɓullo da shi ba, kamar yadda suka alƙawarta kawo wasu hanyoyi na rage raɗaɗi.

Don haka, babu masaniya kan irin tasirin da matakan za su yi idan an ɓullo da su, da kuma uwa-uba sauyin da suka ce za a gani sakamakon cire tallafin man fetur ɗin.

Sai dai ga alama, Musulmai da yawa a Najeriya za su yi fatan Allah ya sa sallar baɗi, ta fi ta bana armashi.

Source: BBC