BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Sinadarin hada lemo na dan tsami ya 'kashe mutum goma a Kano'

 110981580 Cf82acba A3f2 46f4 979f 73dea2b30263 Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje

Sat, 17 Apr 2021 Source: BBC

Gwamnatin jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta tabbatar da cewa mutum 10 ne suka mutu sakamako shan sinadarin lemon dan tsami na jabu.

Kwamishinan lafiya na jihar, Dr Aminu Ibrahim Tsanyawa ya shaida wa manema labarai cewa, binciken da aka gudanar kan bakuwar cutar nan da ta bulla a jihar a makonnin da suka gabata, ya nuna cewa shan sinadarin ne ya haddasa ta.

A cewarsa, fiye da mutum 400 aka kwantar a asibiti sakamakon kamuwa da cutar.

"Shan wadannan sinadarai na da matukar illa ga lafiyar dan adam, yana kuma janyo matsala a koda, da janyo matsala a sassan jikin dan adam, idan da karar kwana har mutuwa mutum zai yi.

Kawo yanzu ma'aikatar lafiya na kula da sama da mutum 400 da suka kamu da matsananciyar rashin lafiya sanadin shan wadannan abubuwa. Sama da mutum 50 ana yi musu wankin koda baya ga mutum sama da 10 da suka mutu," a cewar Dr. Tsanyawa.

"Ganin yanayin zafi da ake ciki, da kuma watan azumin Ramadan da aka fara, akwai yiwuwar za a ci gaba da amfani da wadannan nau'ukan na kayan lemo. Domin haka muke kira ga al'ummar jihar Kano su kiyaye da gujewa ta'ammali da irin wadannan sinadaran na hada lemo," in ji Dakta Tsanyawa.

A kwanakin baya ne dai akai ta kwantar da mutane da dama a asibitocin da ke birnin Kano, sakamakon fitsarin jini da amai da suke yi sakamakon shan lemon da aka hada da sinadarin dan tsami.

Hukumomin jihar sun haramta sayar da sinadarin, suna masu gargadin jama'a su daina amfani da shi.

Kazalika hukumar kare hakkin masu sayen kayan masarufi ta jihar Kano ta sanar da kama mutane hudu da ake zargi da sayar da lemon dan tsami.

Hukumar ta ce an kama mutanen a garin Minjibir da ke Kano, inda aka same su da dan tsami kusan buhu 600, wanda dukkansu lokacin amfani da su ya wuce.

Source: BBC