BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Southampton ta kammala cinikin Sulemana

46643524 Kamaldeen Sulemana

Tue, 31 Jan 2023 Source: BBC

Southampton itama ta shiga kasuwar cinikin yan wasa yan awanni kafin a kulle, inda take tattaunawa da Rennes ta Faransa, don duba yiwuwar kulla cinikin dan wasanta na gefe Kamaldeen Sulemana.

Saints sun cimma matsayar za su biya fam miliyan 22 ga dan wasan na Ghana, a kokarin da suke yi na kaucewa komawa gasar Championship ta Ingila.

Rahotanni sun nuna cewa yanzu haka ana kan gwada lafiyar dan wasan a Faransa.

Sulemana ya tafi Rennes ne daga Nordsjaelland ta Denmark a 2021, kuma kudin da Southampton za ta kashe kansa ya zarta abunda ta kashe wurin sayen Danny Ings a 2019.

Dan wasan mai shekaru 20 ya buga wa Ghana wasanni 15, da suka hada da uku a gasar kofin duniya a ta Qatar 2022.

An yi ittifakin cewa shi ne dan wasan da ya fi kowanne gudu a gasar ta kofin duniya.

Source: BBC