A ranar shida ga watan Mayu ne, za a yi naɗin sarautar Sarki Charles da sarauniya Camilla, a Cocin Westminster Abbey da ke birnin Landan.
Sarkin ya buƙaci a yi bikin nadin sarauta cikin ƙwarya-ƙwaryan taron jama’a, abin da ya sha bamban da nadin sarautar mahaifiyarsa da aka yi a 1953.
An aika takardun gayyata ga mutane kimanin 2000.
Ga abin da muka sani game da mutane da za su halarci bikin a halin yanzu.
Iyalan Masarautar Birtaniya.
Kamar duk wani biki irin wannan, dole a fifita 'yan gida, kuma da yawan iyalan Charles da Camilla, za su halarci bikin naɗin sarautar.
Yarima William Da Gimbiya Catherine, waɗanda su ne yarima da gimbiyar Wales za su halarci bikin, haka ma ‘yan'uwan sarkin guda biyu Gimbiya Anne da kuma Yarima Edward wato yariman Edinburgh.
Bayan doguwar taƙaddama, Yarima Harry ya bada tabbacin cewa zai halarta amma matarsa Meghan ba za ta samu zuwa ba.
Hakan ta faru ne saboda ranar naɗin sarautar ya zo daidai da ranar da ɗansu Yarima Archie yake cika shekara huɗu da haihuwa.
Ana sa ran cewa yariman York, Yarima Andrew zai halarta, amma tsohuwar matarsa gimbiyar York, Sarah Ferguson ba za ta samu damar zuwa ba.
Ana sa ran cewa ‘ya’yansu, Gimbiya Beatrice da Gimbiya Eugenie za su halarci naɗin sarautar a matsayinsu na 'ya'yan sarautar da ke mataki na tara da na 11 a jerin gadon sarautar Ingila- haka ma ɗiyar Gimbiya Anne, Zara Tindall da mijinta Mike Tindall.
Jikokin Sarki Charles da Sauraniya Camilla ma za su halarci bikin naɗin sarautar. Kuma wasu daga cikinsu za su gudanar da ayyuka a lokacin bikin.
Yarima George, ɗan Yarima William da Gimbiya Catherine, wanda shi ne na biyu a jerin masu gadon sarautar, zai kasance ɗaya daga cikinsu.
Jikokin Camilla uku.
Gus Lopez da Louis Lopez da Freddy Parker Bowles da kuma Arthur Elliott su ma za su gudanar da irin wannan aikin, kuma za su kasance cikin jerin gwanon da zai wuce ta gaban Cocin Wetminster Abbey.
Sarauniya Camilla za ta kasance tare da ‘yar'uwarta Annabel Elliot da kuma aminiyarta Lady Lansdowne.
‘Yan siyasa, Shugabanni da Sarakunan ƙasashe
Manyan ƙusoshin siyasa da shugabannin duniya za su kasance cikin jerin mutum 2,000 da za su halarci bikin - kuma ya kamata a san cewa biki ne na gwamnati, kuma ita ce za ta tantance duk waɗanda da za su halarta.
Firaminista Rishi Sunak zai karrama bikin tare da ministoci da kuma ‘yan majalisar dattijai.
Rahotonni sun nuna cewa, tsoffin firaministocin ingila, Liz Truss da Tony Blair za su halarta tare da jagoran gwamnati a Scotland Humza Yousaf.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron zai kasance a wurin bikin. Hakan ya zo ne bayan ɗage ziyarar Sarki Charles zuwa Faransa sakamakon zanga-zangar da aka gudanar a kasar cikin watan Maris, amma wata majiya ta shaida wa ‘The Times’ cewa Mr Macron zai halarci bikin domin ƙara danƙon zumunci da kuma nuna karamci ga Birtaniya.
Shugaban Amurka Joe Biden ya yi magana da Sarki Charles ta wayar tarho a watan Afrilu, inda ya shaida masa cewa ba zai samu damar halartar bikin naɗin sarautar na ranar Asabar ba, amma ya tabbatar da cewa uwargidansa Jill Biden za ta wakilce shi.
Shugaban ƙasar Poland Andrzej Duda da firaminstan Australia Anthony Albanese sun bada tabbacin cewa za su halarci bikin- kuma rahotonni sun nuna cewa firaministan Pakistan Shehbaz Sharif da shugaban Philippines, Ferdinand Marcos duk za su halarta.
An fahimci cewa manyan shugabannin addini da kuma wakilan ƙasashen rainon Ingila wato Commonwealth za su kasance a bikin.
A wani abu da ya saɓa wa al’ada, manyan 'ya'yan sarauta na duniya za su ziyarci birnin Landan domin halartar bikin.
Masu sarautun sun haɗar da Yarima Albert da Gimbiya Chalene na Monaco, da Sarki Felipe da Sarauniya Letizia na Spain, 'ya'yan masarautar Japan kamar Yarima Akishino da Gimbiya Kiko sai kuma sarkin Sweden wato Sarki Carl XVI Gustaf, wanda zai zo tare da ɗiyarsa Gimbiya Victoria.
An samu labarin cewa Shugabar Tarayyar Turai, Ursula Von der Leyen, wadda ta ziyarci Charles a gidan sarautar Windsor cikin watan Fabrairu, za ta hallara a Landan ranar Asabar.
Masu aikin sa-kai da sojoji da ma’aikatan agaji
Sarki Charles da Sarauniya Camilla sun gayyaci wakilan jama'a 850, domin karrama su saboda ayyukan agaji da suke gudanarwa.
Waɗannan sun haɗar da mutum 450 da aka karrama da lambar British Empire da kuma matasa 400 daga ƙungoyoyi daban-daban da iyalan masarautar suka zaɓa.
Wani tsohon ma’aikacin kashe gobara, John Anderson wanda aka karrama da lambar British Empire Medal ya ce an yi matuƙar mutunta shi da wannan gayyata da aka yi masa.
An gayyaci wani matashi, Max Woodsley wanda aka fi sani da laƙabin ‘Yaron da ke cikin tanti‘ wanda ya shekara uku yana kwana a tanti don tara gudunmawar kuɗi ga asibitin ungwarsu.
Sojoji sama da 6000 ne za su gudanar da ayyuka iri daban-daban a bikin naɗin sarautar, abin da ya sa hakan zai zama bikin sojoji mafi girma cikin shekara 70.
An gayyaci dubban tsoffin sojoji da ma’aikatan asibiti ƙarƙashin hukumar inshorar lafiya ta NHS domin su kasance 'yan kallo yayin da bikin ke gudana, an tsara cewa za su zauna a wani dandali na musamman da ke gaban fadar Buckingham.
Hasashe kan halartar wasu fitattun mutane
Ana ta hasashe a kan ko Sarki da Sarauniya za su gayyaci sanannun abokansu zuwa bikin nadin sarautar.
An samu tabbaci kan halartar waɗansu daga cikinsu, dalilin alaƙarsu da Prince’s Trust - wata gidauniyar agaji ta matasa da sarkin ya kafa shekaru da dama a baya. Fitattun ma’aikatan talbijin Ant da Dec waɗanda jakadun gidauniyar ne da suka daɗe suna taimaka mata, su ma za su kasance a Cocin Westminster Abbey.
Za su kasance tare da editan mujallar British Vogue, Edward Enninful da kuma shahararren mawaƙin nan Lionel Richie - dukkansu su ma jakadu ne na gidauniyar Prince's Trust. Haka kuma an gayyaci mutane da yawa daga gidauniyar ta taimakawa a lokacin da su ke matasa- sun hada da mawakiyar ƙungiyar Stereophonics, da kuma Dynamo (Wanda ainihin sunansa Steven Frayne), mai shirin rufa-ido a talbijin.
Sky News sun rawaito cewa Dame Joanna Lumley za ta halarci bikin, kafin ta kasance tare da masu watsa shirye-shiryen bukin.
Duk da yake babu wasu fitattun mutane da suka tabbatar da halartarsu, amma ana sa ran fitattun da ke da kusanci da iyalan masarautar za su kasance a wurin.
Fitattun mutane da dama da suka halarci auren Sarki Charles da Sarauniya Camilla a Cocin St George's Chapel a skekarar 2005, waɗanda suka hadar da shahararrun masu barkwanci Stephen Fry da Rowan Atkinson da kuma jaruman Fim Richard E Grant da Prunella Scales.
Akwai jita-jitar cewa mai yiwuwa David da Victoria Beckham za su halarci bikin. Dukkansu, sun halarci bikin auren Yarima Willaim da Gimbiya Catherine, da kuma auren Yarima Harry da Meghan - kuma tsohon fitaccen ɗan ƙwallon ya bi layi inda ya shafe tsawon sa'a 12 don bankwana da gawar sarauniya.
Amma duk wanda bai yi sa’ar samun takardar gayyata ba, zai iya sauraron shirye-shiryen bikin naɗin sarautar kai tsaye a tashoshin BBC.
Za a iya sauraro a BBC Iplayer da BBC Sounds da kuma sauran kafofin BBC.