Tawagar kwallon kafa ta Najeriya ta tashi 1-1 tsakaninta da ta Rwanda ranar Lahadi a Rwanda.
Tawagogin biyu sun buga wasa na biyu-biyu a cikin rukuni na uku a wasannin neman shiga gasar Kofin Duniya da za a yi a 2026 a Amurka da Canada da Mexico.
A minti na 26 da fara wasa ne Zimbabwe ta fara cin kwallo ta hannun Walter Musona, kuma haka suka je hutu ana cin Super Eagles 1-0.
Bayan da suka koma zagaye na biyu ne Najeriya ta farke ta hannun Kelechi Iheanacho.
Wasa na biyu kenan da Najeriya ta tashi 1-1 a karawar cikin rukuni na uku, bayan da ta yi kunnen doki da Lesotho a Uyo ranar Alhamis.
Ita kanta Zimbabwe ta tashi wasan farko a cikin rukuni da Rwanda ba ci ranar Laraba.
Zimbabwe na buga wasanninta a Rwanda saboda ba ta da filin wasa mai darajar da za a buga wasannin.
Ranar 3 ga watan Yunin 2024 Super Eagles za ta karbi bakuncin Afirka ta Kudu a wasa na uku a cikin rukuni na uku.