Menu

Super Eagles za ta buga wasan sada zumunta duk da fama da rashin kudi

 118575191 Gernotrohr Gernot Rohr, Kocin tawagar kwallon kafar Najeriya

Thu, 20 May 2021 Source: BBC

Najeriya za ta buga wasan sada zumunta da Kamaru da Mexico a Turai da Kudancin Amurka, duk da fama da rashin kudi da hukumar kwallon kafar kasar ke fama.

Kocin tawagar kwallon kafar Najeriya, Gernot Rohr na bin hukumar bashin albashin wata shida da ba a biya shi ba.

Duk da fama da rashin kudi da take fuskanta, NFF ta tsara wasan sada zumunta da Super Eagles za ta kara da tawagar Kamaru a Vienna, Austia ranar 4 ga watan Yuni.

Haka kuma Najeriya za ta kece raini a wasan sada zumunta na biyu da Mexico a Los Angeles a Amurka wata daya tsakani a karawa da Kamaru.

A watan Janairu shugaban hukumar kwallon kafar Najeriya, Amaju Pinnick ya ce yana ta fafutukar ganin ya biya dukkan bashin da ake bin hukumar.

'Yan wasan Super Eagles na bin bashin ladan wasanni da alawus alawus da dama, yayin da mai horar da masu tsaron raga, Alloy Agu ke bin bashin albashin wata 17.

Najeriya ta shirya wasannin sada zumuntar ne don tunkarar karawar neman shiga gasar cin kofin duniya ta 2022 da za ta yi a cikin watan Satumba.

A shekarar bara Rohr ya tsawaita yarjejeniyar ci gaba da jan ragamar Super Eagles da sharadin lashe kofin nahiyar Afirka na gaba da samun gurbin gasar kofin duniya da za a yi a Qatar.

Wannan shi ne wasa na shida da Najeriya za ta fafata da Mexico a manyan karawa, inda hudu daga ciki suka tashi canjaras.

Mexico ta yi nasara a kan Super Eagles da ci 2-1 ranar 24 ga watan Yunin 1995 a US Gold Cup a Texas.

Source: BBC