BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Taliban ta zartar da hukuncin kisa na farko a bainar jama'a

42968003 Ƙungiyar Taliban ta aiwatar da hukuncin kisa a bainar jama'a

Wed, 7 Dec 2022 Source: BBC

Ƙungiyar Taliban ta aiwatar da hukuncin kisa a bainar jama'a da ake tunanin cewa shi ne na farko tun bayan da ta dawo iko da ƙasar Afghaninstan a shekarar 2021.

Mai magana da yawun ƙungiyar ya ce an zartar da hukuncin kisan kan Tajmir a gaban taron al'umma a filin wasan da ke lardin Farah da ke kudu maso yammacin ƙasar, bayan da ya amsa laifin kisan kai da ake tuhumarsa da shi.

Gomman manyan jami'an ƙungiyar, ciki har da manyan ministocin gwamnatin ƙasar ne suka halarci aiwatar da hukuncin.

Lamarin na zuwa ne makonni bayan da aka umarci alƙalan ƙasar da su tabbatar da yin hukunci da shari'ar musulunci a ƙasar.

Jagoran ƙungiyar Haibatullah Akhundzada ne ya bayar da umarnin a watan da ya gabata, yana mai umartar alƙalan ƙasar da su riƙa zartar da hukunce-hukuncen musulunci, ciki har da hukuncin kisa , da hukuncin yanke hannu da na rajamu, duka a bainar jama'a.

To sai dai ƙungiyar ba ta fito ƙarara ta bayyana manyan laifukan da za a iya yanke wa mutum irin wannan hukuncin ba.

Haka kuma ƙungiyar ta alƙawarta dawo da tsauraran hukunce-hukuncen da ta yi amfani da su a baya lokacin da take riƙe da ikon ƙasar tsakanin shekarar 1996 zuwa 2001.

To amma aiwatar da wannan hukuncin -da ƙungiyar ta ce ta aiwatar ranar Laraba, na alamta dawo da tsauraran dokokin da shari'ar musulunci.

Mai magana da yawun ƙungiyar Zabihullah Mujahid, ya ce manyan alƙalan ƙasar, da manyan jami'an soji da wasu ministoci ne suka halarci zartar da hukuncin kisan.

Ƙungiyar ta ce wanda aka zartar wa da hukuncin mai suna Tajmir - ɗa ga Ghulam Sarwar mazaunin lardin Herat - ya daɓa wa wani mutum mai suna Mustafa wuƙa shekaru biyar da suka gabata.

Alƙalan Taliban uku ne suka saurari ƙarar tasa sannan suka yanke masa hukuncin kisan sannan kuma Mullah Akhundzada ya tabbatar da hukuncin.

Kafin zartar da hukuncin an yi yayata batun tare da gayyatar jama'a domin halartar wurin aiwatar da hukuncin.

Mahaifiyar mutumin da Tajmir ya kashe ta shaida wa BBC cewa shugabannin ƙungiyar sun roƙe ta da ta yafe wa Tajmir gabanin zartar da hukuncin, amma ta kafe cewa dole shi ma a kashe shi.

'''Yan ƙungiyar Taliban sun zo waje na tare da roƙa ta da na yafe masa, sun dage cewa na yafe masa dan Allah, to amma na ce musu ba zan iya yafe masa ba dole ne a kashe shi kamar yadda ya kashe min ɗana''.

"Wannan ka iya zama darasi ga sauran mutane, idan ba a kashe shi ba gobe ma zai sake kashe wani," in ji matar.

A lokacin da take riƙe da iko tsakanin 1996 zuwa 2001, an yi ta sukar ƙungiyar saboda yawan zartar da hukunce-hukunce a bainar jama'a, ciki har da hukuncin kisa da take yawan aiwatarwa a babban filin ƙwallon ƙafa na birnin Kabul.

A yanzu dai, babu ƙasar da ta amince da sabuwar gwamnatin ƙasar.

Kuma Bankin Duniya ya riƙe wa ƙasar kusan dala miliyan 600, bayan da ƙungiyar ta rufe makarantun sakandiren mata a faɗin ƙasar.

Haka kuma Amurka ta rufe wasu asusun ajiya na babban bankin ƙasar da ke ƙasashen waje waɗanda ke ƙunshe da biliyoyin daloli.

Source: BBC