BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Tarihin marigayi tsohon firaiministan Italiya Silvio Berlusconi

Tsohon firaiministan Italia, Silvio Berlusconi

Tue, 13 Jun 2023 Source: BBC

Tsohon firaiministan Italia, Silvio Berlusconi, wanda ya tsallake badakalar abin kunya da dama ya mutu yana da shekara 86.

Ya mutu a asibitin San Raffaele na birnin Milan. A watan Afirilu aka yi masa maganin cutar da ta kama huhunsa wadda ke da alaka da kansar jini.

Ministan tsaron Italiya ya ce mutuwar Berlusconi za ta bar babban giɓi, kuma an sanar da zaman makoki a kasar baki daya, ranar Laraba.

Shi ne Firaiministan Italiya da ya fi kowanne dadewa a kan mukamin, tun bayan yakin duniya kuma ya tsallake badakalar mu'amula da mata da kuma rashawa.

Daga shekarar 1994 da ya fara hawa mukamin Firaiminista, hamshakin mai kudin kuma mai kamfanin yada labarai ya jagoranci gwamnatin kasar har sau huɗu ya zuwa shekarar 2011, amma ba a jere ba.

A watan Satumban bara, jamiyyar Berlusconi mai ra'ayin gurguzu ta Forza Italia ta kulla hadaka da Firaiminista Giorgia Meloni.

Da take tsokaci a kan labarin mutuwar tasa, Ms Meloni ta ce za a rika tunawa da shi a matsayin gwarzon namiji.

A wani sakon bidiyo, ta ce marigayin yana daga cikin manyan masu karfin fada a ji, a tarihin Italiya.

Ministan tsaron kasar, Guido Crosetto ya ce: "An kawo karshen wani zamani... Sai wata rana Silvio." a cikin sakon da ya wallafa a Twitter, Mr Crosetto ya kara da cewa mutuwarsa "babban rashi" ne.

Gwamnatin Italia ta ayyana zaman makoki na ƙasa baki ɗaya a ranar Laraba, kuma a ranar za a yi janaizar Berlusconi a mujami'ar birnin Milan.

"Za a yi ƙasa da tutar Italiya da ta sauran ƙasashen Turai a duk gine-ginen gwamnati, daga ranar Litinin," Mr Crosetto ya shaida wa manema labarai.

Shi ma Vladimir Putin ya bayyana Berlusconi a matsayin "abokin kwarai". A cikin wata sanarwa, shugaban Rasha ya ce hikima da jajircewar Berlusconi suna birge shi.

A cikin watan Afirilu likitoci a San Raffaele suka sanar cewa tsohon shugaban Italiyan yana fama da zazzafar kansar jini.

Ya yi ta fama da cututtuka tun bayan kamuwa da korona a shekarar 2020.

Kawo yanzu babu wata sanarwar da hukumomi suka fitar a kan haƙiƙanin abin da ya yi sanadiyyar mutuwarsa.

An haifi Berlusconi a Milan, a shekarar 1936 kuma ya fara da sana'ar sayar da kayan goge-gogen gida, kafin daga baya ya kafa wani kamfanin gini.

Ya zamo ɗaya daga cikin mutanen da suka fi kuɗi a ƙasar Italiya, inda ya kafa kamfanoni da dama, ciki har da gidan talabijin da kamfanin wallafa jaridu da kuma kamfanin tallace-tallace.

Ya kuma ƙara yin fice a duniya bayan ya mallaki ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta AC Milan-ƙungiyar da ya ceto daga tarkon talaucewa a shekarar 1986, kafin ya shiga siyasa a shekarar 1990.

Tsohon ɗan wasa kuma kocin AC Milan, Carlo Ancelotti, wanda a yanzu yake riƙe da Real Madrid ya bayyana Berlusconi a matsayin "mai amana kuma haziƙin mutum mai gaskiya".

Source: BBC