Mai tsaron ragar Barcelona Marc Andre ter Stegen ya yi wasa 23 ba tare da kwallo ya shiga ragarsa ba a La Liga a kakar nan.
Da wannan bajintar ya yi kan-kan-kan da Claudio Bravo, wanda ya yi wa Barcelona wannan kwazon a kakar 2014/15.
Ranar Lahadi Barcelona ta ci Atletico Madrid 1-0 a Camp Nou a wasan mako na 30 a La Liga.
Kawo yanzu Barcelona ta buga karawa 30, saura takwas a kammala kakar tamaula ta Sifaniya ta 2022/23.
Lokacin da Bravo ya yi wasa 23 a La Liga kwallo bai shiga ragarsa, guda 19 aka ci a kakar, yanzu kuma tara ne suka shiga ragar kungiyar Nou Camp karkashin Ter Stegen.
Ter Stergen ya fara da 0-0 a fafatawa da Vallacano ranar 13 ga watan Agusta a wasan farko da bude La Liga ta kakar nan.
Ranar 26 ga watan Afirilu, Barcelona za ta ziyarci Rayo Vallacano, domin buga wasa na biyu a La Liga a tsakaninsu a bana.
Barcelona tana mataki na daya a kan teburin La Liga da maki 76, wadda ta ci karawa 24 da canjaras hudu aka doke ta wasa biyu a bana a La Liga.
Haka kuma kungiyar da Xavi ke jan ragama ta ci kwallo 54 aka zura mata tara a raga a wasannin da ake yi a kakar nan.