Menu

Thiago Silva ya shiga jerin 'yan wasan da suka buga Champions League 100

98624703 Thiago Silva

Wed, 12 Oct 2022 Source: BBC

Ranar Talata Chelsea ta doke AC Milan 2-0 a wasan rukuni na biyar a Champions League da suka a San Siro. Hakan ya sa Chelsea wadda ta doke kungiyar Italiya 5-0 gida da waje a bana ta dare mataki na daya a kan teburin da maki bakwai. Red Bull Salzsburg ce ta biyu da maki shida, sai Milan da Dinamo Zagreb da kowacce tana da maki hurhudu. Mai tsaron bayan Chelsea Thiago Silva ya buga karawar ya kuma zama na baya-bayan nan da ya yi wasa na 100 Champions League. Hakan ya sa ya zama na 47 da suka yi fafata 100 zuwa sama a babbar gasar tamaula ta Turai a tarihi. Mai tsaron bayan Brazil, ya yi wasan farko 20 a AC Miilan, wanda ya fara buga gasar ranar 12 ga watan Satumbar 2009 da Milan ta ci Merseille 2-1. Silva shi ne na biyu da ya buga wasa na 100 a Champions League a kakar 2022/23, bayan Angel Di Maria na Juventus a wasa na biyu a cikin rukuni a bana. Jerin 'yan wasan 10 da suka yi wasa sama da 100 a Champions League 183 Cristiano Ronaldo (Manchester United 59, Real Madrid 101, Juventus 23) 177 Iker Casillas (Real Madrid 150, Porto 27) 159 Lionel Messi (Barcelona 149, Paris Saint-Germain 10) 151 Xavi Hernández (Barcelona) 145 Karim Benzema (Lyon 19, Real Madrid 126) 142 Raúl González (Real Madrid 130, Schalke 12) 141 Ryan Giggs (Manchester United) 136 Thomas Müller (Bayern München) 133 Sergio Ramos (Real Madrid 129, Paris Saint-Germain 4) 131 Manuel Neuer (Schalke 22, Bayern München 109)*

Source: BBC