Tsohon dan wasan Faransa, Thierry Henry ya karbi aikin da zai yi a karo na biyu tare da masu horar da tawagar Belgium da za ta buga gasar cin kofin nahiyar Turai ta bana.
Henry ya yi aikin mataimaki na biyu ga Roberto Martinez a lokacin da Belgium ta buga gasar cin kofin duniya a Rasha, wadda ta kai karawar daf da karshe a 2018.
Henry tsohon dan wasan Arsenal da yake da tarihin yawan ci wa kungiyar kwallaye ya koma mai taimakon Martinez daga baya ya karbi aikin kocin Monaco a Oktoba.
Henry, ya kuma ja ragamar Montreal Impact mai buga gasar kwallon Amurka daga baya ya yi murabus a cikin watan Fabrairu.
Tun farko mai shekara 43 tsohon dan kwallon Barcelona da Monaco yana daga cikin wadanda aka dauka aikin yi wa BBC sharhin gasar cin kofin nahiyar Turai.
Sai dai kuma yanzu ba zai yi aikin sharhin gasar ba, sakamakon horar da Belgium wadda ake sa ran za ta taka rawar gani a kakar bana.
Tawagar kwallon kafa ta Belgium tana rukuni na biyu da ya kunshi Rasha da Finland da kuma Denmark.
Za kuma ta fara wasan farko na cikin rukuni da Rasha ranar 12 ga watan Yuni.