BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Time magazine ya bayyana Messi a matakin gwarzon shekara

72737971 Lionel Messi

Wed, 6 Dec 2023 Source: BBC

Time magazine ta bayyana dan wasan Inter Milan, Lionel Messi a matakin gwarzon dan wasa a duniya a 2023.

Messi, wanda ya koma Miami cikin watan Yuli ya ci kwallo 11 a karawa 14 a dukkan fafatawa, wadda ta lashe League Cup na farko a tarihin kungiyar.

Mai shekara 36 ya lashe kyautar Ballon d'Or na takwas jimilla a cikin watan Oktoba.

Mujallar ta ce Messi ya kara yawan magoya bayan Inter Miami tun bayan da ya koma can, inda aka samu karin masu kallon kungiyar da yawa a fadin duniya.

Cikin wadanda ta karrama sun hada da mai wasan malkwada jiki, Simone Biles da mai linkaya, Michael Phelps da mai kwallon kwando, LeBron James.

Bayan da ya bar Paris St Germain da kwantiraginsa ya kare, Messi ya ce koda yaushe yana kaunar komawa tsohuwar kungiyarsa, Barcelona.

Daga baya sai aka ji ya koma Inter Miami mai buga gasar kwallon Amurka, MLS, bayan da kaka biyu gasar Saudi Arabia ta yi zawarcinsa.

Source: BBC