BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Tinubu ya dakatar da AbdulRasheed Bawa

Shugaban Hukumar Yaƙi da Rashawa da yi wa Tattalin Ariƙin Ƙasa Zagon Ƙasa (EFCC), AbdulRasheed Bawa.

Sun, 18 Jun 2023 Source: BBC

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da shugaban Hukumar Yaƙi da Rashawa da yi wa Tattalin Ariƙin Ƙasa Zagon Ƙasa (EFCC), AbdulRasheed Bawa.

Wata sanarwa da ta fito daga ofishin sakataren gwamnatin Tarayya ta ce shugaban ya ɗauki wannan mataki ne domin bayar da damar gudanar da bincike kan wasu manya-manyan zarge-zargen da ke kan Bawa.

Sanarwar, wadda ta samu sa hannun daraktan yaɗa labaru na ofishin sakataren gwamnatin Tarayya, ta ce an bai wa AbdulRasheed Bawa umurnin miƙa aiki ga daraktan gudanarwa na hukumar, wanda zai kula da yadda za a gudanar da binciken.

Source: BBC