Menu

Tinubu ya umarci kai agaji ga 'yan bikin da jirgin ruwa ya kife da su a Kwara

Shugaba Bola Ahmed Tinubu

Sun, 18 Jun 2023 Source: BBC

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ba da umarnin kai kayan agaji da taimakon da ya wajaba nan take ga mutanen da suka kuɓuta da kuma dangi da iyalan waɗanda suka mutu a hatsarin jirgin ruwan Kwara.

Wata sanarwa da daraktan yaɗa labarai ga shugaban Najeriyar, Abiodun Oladunjoye ta ambato Bola Ahmed Tinubu na cewa ya yi takaicin wannan hatsarin jirgin ruwa da ya kashe mutum 150 a jihar Kwara.

Ya kuma umarci gwamnatin jihar Kwara da sauran hukumomin gwamnatin tarayya da lamarin ya shafa su yi aiki tare don gano sanadi na kusa da na nesa da suka janyo aukuwar hatsarin jirgin ruwan.

Mutanen da hatsarin ya ritsa da su 'yan biki ne da ke komawa gida daga ƙauyen Egbu a cikin ƙaramar hukumar Pategi.

"Ina cike da tsananin takaici game da labarin wannan mummunan hatsari da ya haddasa asarar jama'armu a jihar Kwara" in ji Tinubu.

Tun da farko Mai martaba sarkin Pategi yayin zantawa da manema labarai a Ilorin, babban birnin jihar ya ce gwamnan jihar Abdurraham Abdulrazaq ya kira shi, don yi masa ta'aziyya tare umartarsa ya ci gaba da magana da mutanen yankunan da lamarin ya faru, don taya su juyayi da kuma gano hanyoyin da za a kaucewa sake aukuwar hatsari irin wannan.

A cewarsa, mutanen yankin suna bakin ƙoƙari wajen tsamo sauran gawawwaki da suka nutse a cikin kogi.

Ya ce daga rahotannin da ya samu, injin jirgin ne ya samu matsala lokacin da yake tafiya cikin tsakar daren, abin da ya kai ga kifewar sa.

"Daga rahotannin da muka samu, kimanin mutum 300 ne a cikin jirgin ruwa."

Sarkin ya ce garuruwa huɗu ne a yanki, kuma suna amfani da kogi a matsayin babbar hanyar sufuri.

Rahotanni sun ce jirgin ya kife ne a ranar Lahadi da daddare, inda yake ɗauke da mutane kimanin 300 waɗanda suka fito daga wajen biki.

Wata sanarwa da ta fito daga gwamnatin jihar Kwara ta ce jirgin na ɗauke da mutane waɗanda suka fito daga garin Egboti na jihar Neja a kan hanyarsu ta zuwa Ƙaramar Hukumar Patigi a jihar Kwara.

Sanarwar ta ce mutanen da lamarin ya ritsa da su ƴan asalin garuruwan Ebu da Dzakan da Kpada da Kuchalu da kuma Sampi ne, duk a ƙaramar hukumar ta Patigi.

A lokacin da ya yi magana da manema labarai, Sarkin Patigi, Alhaji Ibrahim Umar Bologi, ya ce bayanan da suka samu sun nuna cewa kimanin mutum 150 ne suka rasa rayukansu, inda aka samu nasarar ceto mutum 53.

Ana yawan samun haɗurran jiragen ruwa a Najeriya, lamarin da kan haifar da asarar rayuka.

Sau da dama akan alaƙanta hakan da ɗaukar mutane a jiragen fiye da ƙa'ida da kuma rashin bin matakan kariya.

Source: BBC