Kungiyar Atalanta ta yi watsi da tayin da Manchester United ta gabatar mata na neman ta ba ta matashin dan wasanta na gaba Rasmus Hojlund, mai shekara 20, inda United ta nemi bayar da kudi da kuma dan wasa, amma kungiyar ta Italiya ta ki yarda da hakan sai dai a ba ta kudi gaba daya. (Athletic )
Al Ahli ta Saudiyya na shirin gabatar da tayin fam miliyan 30 a kan dan wasan gaba na Algeria Riyad Mahrez, mai shekara 32, don raba shi da Manchester City. (Athletic)
Sai dai kuma kociyan Cityn, Pep Guardiola na shirin tattaunawa da Mahrez sakamakon wannan sha'awa da kungiyar ta Saudi Arabia ke nunawa a kansa. (Mirror)
Haka kuma kungiyar Al-Ittihad iata ma ta Saudiyyar na shirin gabatar da tayin fam miliyan 40 a kan dan wasan tsakiya na Liverpool Fabinho, dan Brazil. (Athletic)
Shi kuwa dan wasan tsakiya na Liverpool din Jordan Henderson, na Ingila ya amince da tayin da kungiyar Al-Ettifaq ta Saudiyyar wadda Steven Gerrard ke mata kociya ta yi masa. (Guardian)
Mai yuwuwa Thiago Alcantara na Liverpool ya sake komawa Barcelona a bazaran nan. (Sport)
Ita kuwa Liverpool din watakila ta nemi matashin dan wasan tsakiya na Southampton Romeo Lavia, dan Belgium mai shekara 19. (Mirror)
Aston Villa ta gabatar da tayinta na farko a kan dan wasan gaba na gefe na Bayer Leverkusen Moussa Diaby na Faransa mai shekara 24. (Sky Sports)
Haka kuma Villa na son dan wasan gaba na gefe na Nottingham Forest da Wales Brennan Johnson, mai shekara 22. (Mail)
Manchester United na dab da kammala cinikin da ya kai na fam miliyan 43 da karin fam miliyan 4.3 ta wasu 'yan tsarabe-tsarabe a kan mai tsaron ragar Inter MIlan Andre Onana, na Kamaru. (Fabrizio Romano)
Tottenham za ta gabatar wa Harry Kane, sabon kwantiragin da za ta rinka biyanshi albashin da ya wuce fam dubu 400 a duk mako, sannan kuma za ta ba shi aiki a cikin kungiyar bayan ya daina taka leda, duk saboda ta rike shi saboda Bayern Munich na sonshi. (Telegraph )
Fulham na sa ran doke kungiyoyi irin su Barcelona, Atletico Madrid, Arsenal da Liverpool a kan matashin dan wasan tsakiya na kungiyar Fluminense ta Brazil Andre Trindade, mai shekara 21. (90min)
Nottingham Forest ta yi nisa a tattaunawar da take yi domin sayen dan wasan tsakiya na Ivory Coast Ibrahim Sangare, a kan kudin da ya kai fam miliyan 30 daga PSV Eindhoven. (Football Insider)
Wolves na sha'awar sayen mai tsaron ragar Liverpool Caoimhin Kelleher, dan Jamhuriyar Ireland mai shekara 24, yayin da golan Wolves din Jose Sa dan Portugal ya dauki hankalin Forest. (Mail)
Dan bayan Leeds da Denmark Rasmus Kristensen, mai shekara 26, na shirin tafiya Roma aro, tsawon kaka daya. (Sky Sports)
Chelsea ta yi magana da Lyon domin tattauna cinikin matashin dan wasan gaba na gefe na kungiyar ta Faransa Rayan Cherki, mai shekara 19. (90min)