BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Tottenham ta ƙulla yarjejeniya da Maddison

James Maddison ya koma Tottenham

Fri, 30 Jun 2023 Source: BBC

Tottenham ta ƙulla yarjejeniya da ɗan ƙwallon Ingila, James Maddison a kan fam miliyan 40, inda ya sanya hannu kan zaman shekara biyar daga Leicester City.

Dan wasan mai shekaru 26 ya buga wa Ingila kwallo a wasanni uku sannan yana cikin tawagar da ta lashe kofin FA a shekara ta 2021.

Maddison ya buga wasa 203 a Leicester bayan da kungiyar ta dauko shi daga Norwich a kan fam miliyan 20 a shekara ta 2018.

Ya zura kwallo 10 a gasar Premier a kakar wasan da ta wuce.

Tottenham ta dauko golan Italiya Guglielmo Vicario daga Empoli a Italiya sannan kuma ta kammala kula yarjejeniya da Dejan Kulusevski daga Juventus.

Source: BBC