A ranar 13 ga watan Afrilu ne aka fara azumin watan Ramadan na shekarar 2021 a faɗin duniya.
Musulmai suna shafe wata daya suna azumi na kwana 29 ko kuma 30 a watan Ramadan, daga fitowar Alfijir zuwa faduwar rana.
Amma tsawon sa'o'in azumin ya bambanta daga kasa zuwa kasa, yayin da azumin wasu kasashe bai kai na wasu kasashen tsawo ba.
A lokacin zafi, kasashen da ke arewacin duniya kamar na Turai suna shafe yini mai tsawo kafin su yi buda baki, yayin da wasu kasashen Afirka kuma ke fuskantar matsanancin zafi a lokutan bazara.
A wannan shekarar dai azumi a kasashen duniya ya bambanta daga sa'o'i 10 zuwa sa'a 22.
BBC ta yi nazari kan sa'o'in azumi na wasu kasashen duniya.
Jerin wasu kasashe da tsawon sa'o'in da suke azumi
Greenland ita ce kasar da ta fi ko wacce tsawon sa'o'in azumi. A bana ana azumi na tsawon sa'a 18 ne a ƙasar. Haka ma abin yake a Iceland.
A Rasha ana azumin sa'a 17.
Birtaniya da Faransa na sa'a 16 a bana maimakon 19 a 2018.
China da Libiya da Masar da Moroko da Amurka da Kanada da Afghanista na sa'a 15.
Najeriya da Saudiyya da Indiya da Pakistan da Senegal na sa'a 14.
Afirka Ta Kudu da Tanzaniya da Brazil da Chile da Australia da Indonesiya na shafe sa'a 13.