Menu

Udinese ta naɗa Cioffi sabon kocinta

19773442 Udinese ta naɗa Gabriele Cioffi a matsayin sabon kocinta

Wed, 25 Oct 2023 Source: BBC

Udinese ta naɗa Gabriele Cioffi a matsayin sabon kocinta, domin maye gurbin Andrea Sottil, kamar yadda kungiyar da ke buga Serie A ta sanar.

Kungiyar ta raba gari da Sottil ranar Talata, wanda ya kasa cin wasa da Udinese take ta ukun ƙarshen teburi, bayan buga wasa tara a Serie A kawo yanzu.

''Udinese na sanar da ku cewar ta ɗauki Gabriele Cioffi a matsayin wanda zai ci gaba da jan ragamar ƙungiyar.''

Tuni kociyan ya saka hannu kan yarjejeniyar da za ta ƙarƙare ranar 30 ga watan Yunin 2024 da cewar za a iya tsawaita masa kaka ɗaya.

Cioffi ya sake karɓar jan ragamar Udinese, wadda ya horar a kakar 2021-22.

A kakar da ta wuce ya horar da Hellas Verona, amma aka sallame shi bayan wasa tara da fara kakar da ta wuce.

Source: BBC