Dan wasan tawagar Faransa, Raphael Varane ya sharbi kuka, sakamakon raunin da ya ji a wasan Premier League da Chelsea ranar Asabar. Chelsea ta karbi bakuncin United a karawar mako na 13 a babbar gasar tamaula ta Ingila, inda suka tashi 1-1 a Stamford Bridge. Mai tsaron bayan ya ji rauni, bayan saura kasa da wata daya a fara gasar cin kofin duniya da Qatar za ta karbi bakunci. Varane ya ji raunin ne a kokarin tare Pierre-Emerick Aubameyang na Chelsea, an kuma maye gurbinsa da Victor Lindelof. Kociyan United, Erik ten Hag ya ce ya yi wuri a fayyace girman raunin da ya ji, saboda haka sai likitoci sun auna shi daga nan su bayyana komai. Varane, wanda ya koma Old Trafford da taka leda daga Real Madrid a 2021 na fama da yawan jin rauni a wasannin da yake yi wa United. Chelsea ce ta fara cin United a bugun daga kai sai mai tsaron raga ta hannun Jorginho saura minti uku lokaci ya cika. United ta farke daf a tashi ta hannun sabon dan wasan da ta sayo a bana daga Real Madrid, Casemiro. Chelsea tana mataki na hudu a teburin Premier League a kakar nan da tazarar maki daya tsakaninta da United ta biyar. Za a fara gasar cin kofin duniya ranar 20 ga watan Nuwamba zuwa 18 ga watan Disamba. Faransa ce mai rike da kofin, wadda ta dauka a Rasha a 2018.