BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Varane zai raba gari da Man Utd, Liverpool na son Beier

12184300 Rafael Varane

Mon, 11 Dec 2023 Source: BBC

Raphael Varane zai iya raba gari da Manchester United a Janairu saboda rashin jituwa tsakanin ɗan wasan bayan na Faransa mai shekara 30 da kocin ƙungiyar Erik ten Hag. (Nicolo Schira)

Tottenham ta sha gaban Newcastle a hamayyar sayen ɗan wasan Ingila Samuel Iling-Junior, mai shekara 20 daga Juventus. (Football Insider)

Fulham na matsa ƙaimi kan buƙatar ɗan wasan Le Havre na Senegal Arouna Sangante, mai shekara 21. (Sun)

Fulham na kuma son ɗan wasan Fluminense mai shekara 22, Andre na Brazil. (Nicolo Schira)

Liverpool na cikin ƴan wasan Premier na farautar matashin ɗan wasan Jamus mai shekara 21 Maximilian Beier, wanda ake sa ran zai bar Hoffenheim a bazara. (Sky Sports Germany)

Everton a shirye take ta sayar ɗan wasan baya na Ingila Ben Godfrey, mai shekara 25 ga Tottenham a Janairu. (Football Insider)

An yi wa Manchester United tayin lunka albashin ɗan wasan Barcelona mai shekara 24 Ronald Araujo, wanda ba ya nuna rashin buƙatar zuwa Bayern Munich. (Mundo Deportivo - in Spanish)

Ɗan wasan gaba na Faransa Mathys Tel, mai shekara 18, ya yanke shawarar ci gaba da zamansa a Bayern Munich akalla zuwa baɗi, duk ƙungiyoyi da dama sun nuna buƙatar karɓar aronsa, har da Manchester United. (Sky Sports Germany)

Chelsea ta shiga tattaunawa da Palmeiras kan ɗan wasan gaba na Brazil mai shekara Estevao Willian, da ake kira 'Messinho', wanda Barcelona ta nuna sha’awarta.. (Goal, via Mundo Deportivo - in Spanish)

Kocin Arsenal Mikel Arteta ya gayyaci tsohon fitaccen ɗan wasan ƙungiyar Dennis Bergkamp ya dawo ƙungiyar domin zama daya daga cikin masu horar da tawagar matasan ƙungiyar. (Football Transfers)

Source: BBC