Menu

Wane ne ke da iko a Iran?

78673487 Masu zanga zanga da ke rike da hoton Ayatolah da baban sojar Qasim Soleimani

Fri, 14 Oct 2022 Source: BBC

Jami'an tsaro sun tsaurara matakan murkushe masu zanga-zangar da ta barke a kasar bayan mutuwar wata matashiya a da aka tsare. An kama Mahsa Amini, mai shekara 22, aka kuma tsare ta saboda kin ruwa kanta sosai da dan kwali ko hijabi. A kan haka ne zanga-zanga ta barke a fadin kasar, inda masu rajin kare hakkin dan-Adam suka ce an kashe akalla mutum 150. To wane ne ke yanke hukuncin lokacin da za a yi amfani da karfin tsiya wajen murkushe maso zanga-zanga? Mene ne karfin ikon jagoran addinin kasar? Mutumin da ya fi kowa iko a Iran shi ne Ayatollah Ali Khamenei, babban jagoran addinin kasar tun 1989. Shi ne jagoran kasa kuma babban kwamandan tsaron kasar. Yana da iko a kan rundunar 'yan sanda da kuma jami'an Hisbah na kasar, wadanda su ne suka kama Mahsa Amini. Ayatollah Khamenei ne kuma yake da iko a kan Rundunar Sojin Juyin Juya Hali ta kasar, wadda ita ce ke kula da harkokoin tsaro na cikin gida, tare kuma da bangarenta na sojin sa-kai (Basij). Wannan runduna ta sojin sa-kai ta sha murkushe tarzoma da zanga-zangar kin jinin gwamnati a Iran. Saboda haka jagoran addinin shi ne ya fi iko a kan yadda za a bullo wa zanga-zangar. Wane iko shugaban kasar yake da shi? Shugaba Ebrahim Raisi, shi ne babban jami'i zababbe kuma na biyu bayan babban jagoran addinin. Shi ne ke da alhakin gudanar da ayyukan yau da kullum na gwamnati kuma yana da tasiri sosai a kan manufofin kasar na cikin gida da kuma waje. Sai dai kuma duk da haka ana iya cewa ikonsa yana da iyaka musamman idan ana maganar harkokin tsaro. Ma'aikatar harkokin cikin gida ta shugaban kasar ita ke tafiyar da rundunar 'yan sandan kasar, wadda ke kokarin murkushe masu zanga-zanga. To amma kuma babban jagoran addinin kasar ne ke nada kwamandan 'yan sandan, kuma a karkashinsa yake kacokan. Haka shi ma kwamandan rundunar sojin juyin-juya-hali da kuma bangaren wannan runduna na sojin sa-kai wato Basij duk suna karkashin ikon babban jagoran addinin ne. Idan har babban jagoran addinin kasar yana son a yi amfani da karfi wajen murkushe masu zanga-zanga, to fa shugaban kasar ba shi da wani zabi illa ya bi hakan. Haka kuma majalisar dokoki, wadda ta bullo da wasu sabbin dokoki za ta iya kawar da ikon shugaban kasar. Sai dai Majalisar Shura, wadda ta kunshi makusantan babban jagoran addinin, ita ke da ikon amincewa da sabbin dokoki, kuma tana da damar kin amincewa da su. Su waye 'yan Hisbah? Jami'an Hisbah wani bangare ne na rundunar 'yan-sandan kasar ta Iran. An kafa su ne a shekara ta 2005 domin tabbatar da mutane na sanya tufafi kamar yadda dokokin mUsulunci suka tanada, dokar da aka bullo da ita a kasar bayan juyin-juya-hali na Musulunci a 1979. Jami'anta da aka yi kiyasin sun kai 7,000 da suka kunshi maza da mata , suna da ikon yi wa mai laifi gargadi ko cin tara ko kuma kamawa. Shugaba Raisi, mai tsananin ra'ayin rikau ya bullo da sabbin matakai na tilasta amfani da hijabi a bazaran nan. An kakkafa na'urorin daukar hoto da za su gano matan ba sa bin dokar sanya hijabin a tituna da sauran wurare. Kuma an yi dokar tura duk mutumin da aka kama yana adawa da dokar sanya hijabin a shafukan intanet. Su waye sojojin juyin-juya-hali? Rundunar sojin juyin-juya-hali ta Iran ita ce ke aikin tabbatar da tsaro a cikin gida. An kafa ta ne bayan juyin-juya-halin domin ta tabbatar da tsarin dokokin Musulunci da kasar ta zaba. A yanzu wannan runduna mai matukar tasiri ta kunshi harkokin soji da siyasa da kuma tattalin arziki a Iran, inda take da sama da jami'ai dubu 150. Tana da sojojin kasa da na sama da kuma na ruwa, sannan ita ke kula da muhimman makaman kasar ta Iran. Haka kuma tana da reshenta na waje da ake kira Quds, wadda a cikin sirri take samar da kudade da makamai da fasaha da kuma horas da abokanta a fadin Gabas ta Tsakiya. Bugu da kari ita ke tafiyar da harkokin reshenta na sojin sa-kai wato Basij. Mene ne Basij? Rundunar Basij da farko an kafa ta ne domin taimaka wa marassa galihu ko wadanda ake yi wa danniya, inda aka samar da ita a shekarar 1979, a matsayin rundunar 'yan sa-kai. Tana da rassa a dukkanin larduna da birane na Iran da kuma cikin da yawa daga hukumomin kasar. Ana kiran mambobinta da suka kunshi maza da mata ''Basijis'', wadanda ke biyayya tare da karbar umarni daga Rundunar Sojin Juyin-Juya-Hali. Ana ganin kusan mambobin rundunar dubu 100 na gudanar da ayyukan tabbatar da tsaro a cikin kasar. Suna taka rawa sosai wajen murkushe zanga-zangar kin jinin gwamnati tun bayan zaben shugaban kasar na 2009 da aka yi takaddama a kansa.

Source: BBC